✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda muka yi arba da barayin waya

Bayan na sauka daga mota a dai-dai Tashar ’Ƴankaba, na tare Keke NAPEP wanda akwai mutum biyu a ciki, nace masa Kwari kuma ya amsa…

Bayan na sauka daga mota a dai-dai Tashar ’Ƴankaba, na tare Keke NAPEP wanda akwai mutum biyu a ciki, nace masa Kwari kuma ya amsa da na shiga.

Ban dade da shiga ba daya daga cikinsu ya ce wa direban NAPEP din ka ji inda ya ce zai je? Sai ya juyo ya ce ba Dakata ya ce ba? Dayan ya ce a’a Kwari ya ce.

Kawai sai ya tsaya, fitowata ke nan na taba aljihun gefena na ji ba waya; Cikin ikon Allah, ya murza NAPEP zai ware, na rike ta da fadin ‘wait’.

Na gefen da na zauna yana ganin haka ya saki wayar a wurin da na zauna ya basar, na dauki wayata suka kara gaba, ba um ba um ummm.

Tabbas na auna arziki, domin duk wanda na fada wa abin da ya faru yakan yi mamaki da ba su zaro makami sun tafi da ita  (wayar) ta karfi ba.

Ko don ni inda suka dauke ni kuma suka sauke ni bayan zare wayar a cikin mutane ne, wanda in suka yi wani yunkuri za su iya dibar kashinsu a hannu, domin dama mutane a kule suke kan yawaitar sata da kwacen waya.

Matsalar satar waya a babura masu kafa uku ya zama tamkar ruwan dare gama duniya, wanda ya mamaye kowane lungu da sako na birnin Kano, inda a kullum sai an samu rahoton sane da kwacen wayoyi.

Ta kai ga har mutane fargaba suke yi su fita da manyan wayoyinsu daga gidajensu, domin ba su da tabbacin dawowa da su ba a kwace ko an sace ba.

Dole ne jama’a su kara yin taka tsantsan da lura wajen hawa ababen hawa, domin da yawa bata-gari ne ke tuki a kan tituna. Hausawa na cewa ‘taya Allah kiwo ya fi Allah na nan’.

Sace-sacen wayoyi ba zai rasa nasaba da yawaitar matasa masu shan miyagun kwayoyi ba, domin yawancin barayin ’yan shaye-shaye ne da idan suka sace suke zuwa su sayar a kan farashi mai rahusa domin samun na sayen kayan mayensu.

Dakile safara da shan kayan maye ba iya sata da kwacen wayoyi zai rage ba, har ma da aikata muggan laifuka.

Haka kuma matsalar ba za ta rasa nasaba da dimbin matasan da ke zaman kashe wando babu sana’o’in dogaro da kai ba, wadanda kullum burinsu shi ne su ci bulus ko bagas.

Dole ne masu hannu da shuni da hadin kan gwamnati su bullo da tsare-tsaren sana’o’in da za su rage matasa zauna-gari-banza a kan tituna.

Haka kuma matsalar ta yi kamari ne saboda rashin zartar da hukunci ga wadanda ake kamawa, duk da cewa gwamnati da jami’an tsaro na nasu kokarin.

Amma tabbas ya kamata su rubanya kokarin wajen shawo kan wannan ta’addanci tun kafin lamarin ya gagari Kundila.

Daukar tsattsauran mataki ga duk wanda aka kama ya yi kwace, sane ko satar waya ne kadai zai yayyafa wa lamarin ruwa, domin tuni mutane da yawa suka rasa rayukansu a kan raba su da wayoyinsu.

Allah Ya shiryar da matasanmu, Ya ganar da su hanya madaidaiciya. Amin

Daga: Aminu Ibrahim
0803661638
[email protected]