✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muka tsere wa tsara a Najeriya -Kamfanin Boulos

Aminiya: Za mu so ka gabatar mana da kamfaninku? Stanley Ebans: Kamfanin Boulos Enterprises Limited an kafa shi tun shekarar 1964. Mun kware wajen harhada…

Aminiya: Za mu so ka gabatar mana da kamfaninku?

Stanley Ebans: Kamfanin Boulos Enterprises Limited an kafa shi tun shekarar 1964. Mun kware wajen harhada babura masu kafa biyu da masu uku. A takaice dai muna wakiltar kamfanoni biyar da suka yi fice wajen kera babura a duniya, su ne kamfanin Suzuki da Piaggio da Haojue da kuma robbinson wadanda suka yi fice wajen kera baburan tsere da na hawa da babura masu taya uku na daukan jama’a da kuma masu daukan kaya da kuma injin jirgin ruwa. Duk mu ne muke hada su a nan Najeriya mu sayar da su ga dimbin abokanen huldarmu.
Aminiya: Ka ce shi ne kamfani daya tilo da gwamnati ta bai wa damar shigo da inji mai salo hudu da a turance ake kira Four-stroke. Ta yaya kuka samu wannan dama?
Stanley Ebans: Mun cimma haka ne saboda jajircewa da mayar da hankali wajen cimma burin da muka sanya a gaba. Dadewar da muka yi muna hadin gwiwa da kamfanin Suzuki da ke kasar Japan ita ma ta taimaka kwarai da gaske wajen cimma wannan buri. Ka san kamfanin Boulos shi ne kamfani na farko da ya fara shigo da baburan Suzuki. Shi ya sa muka kudurce mu ci gaba da samar wa da jama’a Babura masu inganci wadanda suka dace da yanayin muhallin Najeriya. Mun ji dadi da gwamnati ta ba mu wannan dama na shigowa tare da sayar da inji mai salo hudu a kasar nan. Kada ka manta shi injin mai salo hudu inji ne da yake da tattali fiye da kashi 50 cikin 100 idan ka kwatanta shi da inji mai salo biyu.
Aminiya: Me ye ya bambanta baburanku da baburan sauran kamfanoni da suke gogayya da ku?
Stanley Ebans: Dukkanin baburanmu sun sha bamban da sauran baburan abokanen takararmu a kasuwa. Ka dauki misali da babur din Elegant mai karfin 125. Za ka ga ya bambanta da babur din kasar Indiya wanda ake kira Bajaj mai karfin inji 100 ta fannonin da yawa kamar kirkira da salon giya da makunna da batiri da wurin kulle kan babur da tsarin taya da wurin zaman fasinja da gejin mai da karfin inji da fitila gaba da asali da tsari da kuma farashi. Babur din Elegant yana da babban inji fiye da Bajaj, yana da giya biyar a maimakon giya hudu irina Bajaj yana da makunna mai sarrafa kanta da mai tashin babur, amma Bajaj makunna kawai yake da shi. Elegant yana da karfin mataki na 7 amp shi kuwa Bajaj karfin mataki 2.5 amp yake da shi. Wannan shi yake nuna cewa babur dinmu zai fi dadewa idan aka kashe shi sannan kuma ya fi kwanciyar hankali a lokacin gaggauwa. Na mu yana da gejin mai, amma Bajaj ba shi da gejin mai. Duk da cewa ana sayar da namu naira dubu 116 shi kuwa Bajaj ana sayar da  Naira dubu 125, namu an fi samun kayan gyaransa kuma ya fi karko.
Aminiya: Ta wadanne hanyoyi kuke gamsar da abokanen huldarku?
Stanley Ebans: Kamfanin Boulos ba kawai ya takaita a saye da sayarwa kawai ba, amma yana mayar da hankali wajen gamsar da abokan huldarsa ta yadda za su ci gaba da hulda da shi ta har abada. Saboda haka muna da hajoji da aka kirkira don biyan bukatar abokenan huldarmu. Muna ba da muhimmanci ga tallafawa wanda ya sayi kayanmu ta hanyar sama masa kayan gyara masu inganci. Hakan ya kara dankon huldarmu da abokanen cinikinmu a sassa da dama na kasar nan. Ina mai tabbatar maka da cewa muna tsari mai inganci na dillolinmu don samar wa abokanen huldarmu kayanmu a kasuwa.
Aminiya: Wutar lantarki na daga cikin kalubalen da ke ci wa kamfanoni tuwo a kwarya a Najeriya, ta yaya hakan ya shafi ribar da kuke samu da kuma farashin kayanku a kasuwa?
Stanley Ebans: Hakikanin gaskiya wutar lantarki tana da muhimmanci ga harkokinmu na yau da kullum to amma idan da a ce za mu rika samun wutar lantarki ba tare da yankewa ba da mun ji dadi. To amma a duk lokacin da muka samu kanmu a rashin wutar lantarki, sai mu yi amfani da ta mu wutar da muka samar daga sashenmu na yin takardar bandaki. Babu shakka karancin wutar lantarki ya shafi wani kaso na kudin da muke gudanar da harkokinmu na yau da kullum. Kuma wannan shi ne kalubalen da kamfanonin suke fama da shi a Najeriya.
Aminiya: Kwanannan kamfanin Boulos ya yi ikirarin cewa yana fadada harkokinsa, to yaya wannan batu yake?
Stanley Ebans: Abu na gaba da muka yi dangane da fadada harkokinmu shi ne na samar da sabuwar kira ta babur din tsere kirar Aprilla da babur din motor-Guzzi wanda kamfanin Italiya yake kerawa. Banda wannan za mu fara hada babur mai taya uku kirar kamfanin Piaggio mai suna Piaggio Cargo. Saboda haka muna fadada harkokinmu don mu dadadawa abokanen huldarmu tare kuma da ci gaba da kasancewa jagora a kasar nan.
Aminiya: Kuna da tsari na fadada kasuwancinku a yankin Arewacin kasar nan? 
Stanley Ebans: Babu shakka muna da tsare-tsare da yawa dangane da Arewacin Najeriya, amma ya danganta da yadda kasuwar take. Mun dade muna amfani da damar da muka samu wajen sayar da kayayyakinmu a Arewa kamar babur din Piaggio mai taya uku da babur kirar Haojue. Muna kara samun karbuwa a yankin Arewa ta hanyar sayar da kayyakinmu a yankin.
Aminiya: Kwanannan janar manajanku, Mista Julian Hady, ya ce kamfanin Boulos ya amince da bin doka da oda wajen gudanar da harkokinsa, to ta yaya kuke cimma nasara ganin cewa wasu da dama suna ganin ba za a ci gaba ba sai an karya doka a Najeriya?
Stanley Ebans: Gaskiya ne mun mun yi imani da bin doka da oda. Duk abin da za mu yi ba ma bi ta bayan gida. Mun dade a Najeriya, mun yi fiye da shekaru 50 muna kasuwanci a Najeriya. Mun tsaya da gidinmu kuma kafuwar da muka yi ita ta bamu damar tun karar duk wanu kalubale a lokacin tsanani. Mun yarda da ma’aikatanmu kuma hakan ya sanya muna cimma nasarori masu yawa. Muna da hajoji da kayayyaki da yawa. Idan muka fuskanci kalubale a wata haja tamu, sai mu sanya wata hajar a kasuwa sai ka ga komai ya tafi daidai.
Aminiya: Ta yaya kuka kafu duk da kalubalen rashin tabbas a harkokin kasuwanci a kasar nan musamman ma wajen farashin kaya?
Stanley Ebans: Kayanmu yana da arha idan aka kwatanta da abokanen gogayyarmu. Muna samar da kaya masu inganci da arha. Kuma kayanmu sun dace da muhalli kuma ba sa cutarwa ga dan Adam. Muna da kayayyaki masu inganci kuma masu saukin mu’amala. Dalilin da ya sa ake ganin muna iya fuskantar duk wani kalubale shi ne muna hada baburanmu a nan kasar nan don mu sayar da su arha ga abokanen huldarmu.