Farin cikin Mista Nonso Amyaegbu ba zai misaltu ba lokacin da matarsa, Mauree mai kimanin shekaru 41 ta haifa masa ’yan hudu rigis, shekaru biyar bayan aurensu.
Ta haihu ne a asibitin gwamnatin tarayya na Ebute-Meta da ke Yaba a Jihar Legas.
A cewar Mista Nonso, an samu karuwar ne ranar 6 ga Agusta bayan wata tiyata da kimanin jami’an lafiya 20 suka jagoranta na kusan tsawon sa’a bakwai.
Ya ce daga cikin jariran da aka haifa, uku mata ne sai kuma namiji daya. “An shiga da matata dakin tiyata da misalin karfe bakwai na safe amma ba su fito ba sai wajen karfe 1:30 na rana.
“Na yi ta addu’a lokacin da suke ciki saboda na tsorata da farko, kai akwai lokacin da ma sai da fargabar da nake yi ta so ta rinjayi murnar samun ’ya’yan saboda halin da ta tsinci kanta a ciki,” inji Mista Nonso.
Ya ce bai taba tunanin matar tasa ’yan hudu za ta haifa ba sai bayan tiyatar saboda kusan duk sakamakon hoton awon ciki ’yan uku ya rika nuna musu.
Da yake tsokaci a kan lamarin, likitan da ya jagoranci tiyatar wanda kuma kwararre ne a bangaren mata, Dakta Job Adebayo ya ce matar ta yi ta samun kulawa tun lokacin da ta dauki cikin har zuwa haihuwarta.
Ya ce sai da suka ware sashe guda a asibitin saboda yawan ’ya’yan da ta ke dauke da su.
“Lokacin da nake tiyatar bayan ciro jariri na uku, saura kiris na cire safar tiyata kwatsam sai na ji alamar motsi, ashe akwai na hudu a ciki.
“Kai a takaice, jariri na hudunma duk ya fi ragowar ukun nauyi. Dukkansu su na cikin koshin lafiya,” inji likitan.
Mahaifin yaran ya nuna godiyarsa ga Allah kan baiwar, inda ya ce shi da matarsa tasa sai da suka shekara biyar da aurensu kafin samun rabon.
Ya ce sun fuskanci matsananciyar damuwa sakamakon rashin samun haihuwa da wuri, amma daga bisani ya yi kokari ya kwantar wa matar tasa da hankali.
“Shekaru biyu bayan aurenmu ba haihuwa sai muka fara neman magani da shawarar likitoci, amma aka tabbatar mana lafiyarmu kalau.
“Haka dai muka ci gaba da neman magani da addu’o’i har Allah Ya amsa addu’armu.
“Da addu’ar da ko guda daya muke yi, sai Allah cikin ikonSa Ya ba mu hudu”, inji shi.
Mahaifin ’yan hudun wanda kwararre ne a harkar tsara gine-gine ya ce ya yi matukar mamaki lokacin da aka ce masa an samu ’yan hudu sabanin ’yan ukun da hoton awon ciki ya sha nuna musu.
Ya ce yanzu haka yaran suna asibiti suna samun kulawa yayin da matar tasa ita ma ke kara murmurewa.
Ya shawarci ma’auratan da suka samu tsaiko wajen haihuwa da su ci gaba da addu’a da hakuri kuma kada su yi watsi da shawarar likitoci, tare da kira ga gwamnati da ta tallafa masa wajen kula da su.
Ita kuwa mai jegon, Misis Maureen wacce ma’aikaciyar gwamnati ce ta gode wa mijin nata saboda taimako da kwarin gwiwar da ya ba ta lokacin suna jiran haihuwar tsawon lokaci.