✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Yadda mijina ya gudu ya bar ni a asibiti saboda haifa masa tagwaye’

Ta ce hatta wadataccen abinci ma wahala yake yi musu tsawon wannan lokacin.

Wata mata mai kimanin shekara 24 a duniya mai suna Abibat Kehinde ta yi zargin cewa tsawon wata uku kenan mijinta ya gudu ya barta a asibiti saboda ta haifa masa tagwaye.

A cewarta, mijin nata, wanda dan acaba ne ya gudu ya barta da bashin N131,000 a Babban Asibitin Epe da ke Jihar Legas tsawon wannan lokacin.

Abibat ta shaida wa Kamfanin Daillancin Labarai na Najeriya (NAN) ranar Juma’a cewa mijin ya gudu ne tun bayan da ta haifi tagwayen a ranar 21 ga watan Maris na 2021 ba tare da ya biya kudin sallamarsu daga asibitin ba.

Ta ce, “Ya gudu ya barni tun da na haifi tagwaye ranar 21 ga watan Maris.

“Ba laifina ba ne haihuwar tagwayen, amma Allah ya fini sanin gaibu,” inji ta.

Ta ce hatta wadataccen abinci mai gina jiki wahala yake yi mata ita da jariran tsawon wannan lokacin.

“Mijina ya ce ko jariri daya bashi da karfin ciyarwa, ballantana tagwaye da mahaifiyarsu, kuma ya koka matuka a kan yawan kudin asibitin.

“Tun da ya bar asibitin a lokacin bai sake ko dawowa ya waiwaye mu ba.

“Na yi kokari na samo N30,000 daga kudin asibitin na N161,000, yanzu ana binmu N131,000 kenan.

“Tun watan Maris nake a asibitin nan ba tare da an sallame ni ba.

“Kullum kudin sai karuwa yake yi gashi ni kuma bani da hanyar biyansu,” inji ta.

Daga nan sai ta roki hukumar asibitin da ta taimaka ta sallameta da ita da tagwayen nata.

Jami’in kula da walwala na asibitin, Ayanbisi Rauf ya tabbatar da cewa mijin matar ya gudu ya barta.

“Ya gudu ya barta tsawon watanni uku kuma duk kokarin hukumomin asibitin na gano inda yake ya ci tura,” inji shi.

Sai dai ya ce za su iya barinta ta fice daga asibitin ne kawai in ta iya biyan akalla kaso 90 cikin 100 na kudaden.

Ya yi kira ga daidaikun mutane masu hannu da shuni da sauran kungiyoyi masu zaman kansu kan su taimaka mata wajen biyan kudaden domin ta samu a sallameta. (NAN).