✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matashiya ta kashabe yayanta da wuka akan wakar biki

Rundunar ‘yan sanda jihar Kano ta kame wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Mariya Sulaiman, da ake zargi da laifi kashe yayanta Sani Sulaiman…

Rundunar ‘yan sanda jihar Kano ta kame wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Mariya Sulaiman, da ake zargi da laifi kashe yayanta Sani Sulaiman mai shekaru 30 biyo bayan gardamar da ta kaure a tsakanin su a kan wakar da za a sa a lokacin bikin ‘yar uwar su a karshen makon da ya gaba ta.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Haruna Abdullahi ya shaida cewa, lamarin ya faru ne a unguwar Badawa da ke Karamar Hukumar Nasarawa a jihar Kano, ya ce gardama ce ta kaure a lokacin da ake bikin auren yayar wace ake zargin, lokacin da marigayin ya ce a cire wata waka a sauya ta da wata sai kanwarsa ta yi kememe ta ce atafau baza a sauya wakar ba inda nan take ta daba masa wuka a wuya.

Kwamishinan ‘yan sanda Kano Ahmed Iliyasu, ya bada umarnin bincikar lamari, Majiyar mu ta shaida cewa mahaifin yarinyar Alhaji Sule Ustaz, da mahaifiyarta sun sume a lokacin da suka ji labarin ta kashe dan uwanta lamarin da ya sanya aka garzaya da su asibiti.