Yawan manyan jami’an gwamnati da ke kamuwa da cutar coronavirus a Najeriya sai karuwa yake yi, lamarin da ya fara daga hankalin sauran masu fada-a-ji.
Ko ranar Litinin ma, Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma shugaban kwamitin kar-ta-kwana da shugaban kasa ya kafa don yaki da cutar, Boss Mustapha, ya nuna irin wannan damuwa yayin jawabin kwamitin a Abuja.
“Wannan cutar ba ta nuna bambanci tsakanin jama’a, saboda haka ne kwamitinmu ke yin duk mai yiwuwa wajen ci gaba da wayar da kan al’umma”, inji Boss Mustapha.
Cutar dai ta yi sanadiyyar rayukan Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Abba Kyari da kuma tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi da kuma dan majalisar dattawa Sanata Sikiru Adebayo Osinowo.
Kazalika, gwamnonin jihohin Kaduna, Bauchi, Oyo, Ondo da kuma Abia masu ci duk sun kamu da cutar kafin daga bisani su warke.
Cikas ga harkokin mulki
Sakataren gwamnatin ya ce yadda manyan jami’an ke kamuwa na kawo cikas ga tafiyar da harkokin mulki da ma na tsaron kasa.
Ya ce yayin da kasar ke shirye-shiryen aiwatar da zango na biyu na sassauta dokar kulle, gwamnati za ta ci gaba da sa ido wajen tabbatar da an bi dokokin yadda ya kamata musamman a wuraren taruwar jama’a.
“Na san wasu za su yi wa wannan matakin gurguwar fahimta cewa an kammala yaki da wannan annobar, amma mun dauki wannan matakin na sassauci ne don mu ba mutane damar ci gaba da rayuwarsu”,inji shi.
Mustapha ya ce yadda ake kara samun sabbin kamuwa da cutar a fadin duniya na nuna cewa har yanzu akwai jan aiki a gaban kasar kuma bai kamata su yi kantafi da rayuwar mutane ba.
Ya kuma ce a ranakun Alhamis da Juma’a masu zuwa kwamitin zai gudanar da nazari kan aikace-aikacensa kasancewar ya haura adadin wata ukun da aka debar masa tun da farko.
Ya ce nazarin zai kunshi zuzzurfan bincike kan matakan da suka dauka, kalubalen da suka fuskanta da kuma inda za a dosa a nan gaba.
Dalilin da ya sa cutar take kama su —Masana
To ko yaya masana harkar lafiya ke kallon yanayin kamuwar manyan mutanen?
Dakta Ibrahim Musa, wani kwararren likita a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano ya ce kamuwa da cutar ba shi da alaka da matsayin mutum a cikin al’umma.
“Ni ban yarda wai cutar ta fi kama manyan mutane ba. Talakawa, attajirai, masu mulki da duk wani sashe na jama’a na kamuwa da ita”, inji Dakta Musa.
Ya kara da cewa, “A Najeriya alal misali, kusan mutum 30,000 sun kamu yanzu haka, amma manyan mutane nawa ne a cikinsu?
“Ni abun da na fi tunani shi ne ku ‘yan jarida kun fi yayata labarin idan ta kama manyan mutane, amma hakan ba yana nufin cewa ta fi kama su ba ne.
“Ya kamata kuma mu lura cewa wadannan rukunin mutanen sun fi samun kulawa ta lafiya, watakila shi ya sa ake samun masu ita a tsakaninsu.
“Mai yiwuwa ne a cikin wasu talakawan ma wasu sun yi sun warke ba su sani ba saboda ba su samu damar a gwada su ba”, a ta bakin likitan.
Masanin harkar lafiyar ya kuma ce la’akari da cewa manyan mutanen kamar sauran jama’a su ma suna mu’amala tare da karya dokokin, ba abin mamaki ba ne don su ma ta kama su.