✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mai gadi ya sa dansa makaranta har ya samu digirin-digirgir

Salisu Bala ya samu digirin digirgir (PhD) yana matashi dan shekaru 39 daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. A yanzu babban ma’aikaci ne a Gidan Marigayi…

Salisu Bala ya samu digirin digirgir (PhD) yana matashi dan shekaru 39 daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. A yanzu babban ma’aikaci ne a Gidan Marigayi Saudauna (Arewa House), Kaduna sannan kuma yana koyarwa a Sashin Tarihi na jami’ar da ke Zariya.

Salisu Bala an yi mai kamun kazan-kuku ne, inda mahaifinsa ya kama hannunsa ya ce mu je. Ganin an tsallaka titi mai yawan motoci na Ali Akilu, sannan aka ka ishi inda ake ta zabga masa tambayoyi, sai ya barke da kuka, da kyar ya fadi sunansa ya ce “Salisu.” Sai mahaifinsa ya ce “Salisu Bala,” watau lakanin Salisu. Amma ba sunan mahaifinsa ke nan ba, sunan mahaifinsa Jibril Haruna wanda aka fi sani da suna Zariya. Bayan ya taba kunnensa na hagu da hannunsa na dama sai aka ba shi aji ‘1E’ a Makarantar Sultan Bello a Unguwar Sarki, Kaduna.
Jibril Haruna Zariya (mahaifin Salisu), ma’aikaci ne a Gidan Adana Kayan Tarihi na Sardauna da ke unguwar Sarki Kaduna, wanda ke karkashin Jami’ar Ahmadu Bello Zariya. Salisu Bala ya fi kowa murna lokacin da aka ba shi sabon kayan makaranta mai alamar tutar Najeriya sannan aka hada su a aji daya da yayansa wanda yake gaba da shi da shelaru 6, inda ya rika kare shi daga masu cin zali da kuma tsallake titi don zuwa makaranta. Salisu Bala ne dan autan ajin don ya fi karancin shekaru.
A lokacin, in ji Salisu Bala, ajinsu daya da ’ya’yan Mataimakin Gwamnan Kaduna, wanda kuma daga baya ya zama Gwamna, wato Abba Musa Rimi, bayan zamanin Balarabe Musa. A lokacin makarantu gwamnati suna aiki sosai don ba makarantu masu zaman kansu. Domin ’ya’yan masu hali da talakawa, makarantar suke zuwa. Yawancin sakamakon jarabawansa yana daukar mataki na tara ne zuwa na goma. Amma wansa yana daukar na biyu zuwa na uku a aji mai dalibai talatin. Kuma ya fi son fannonin lissafi da zamantakewar dan Adam. Kuma malaman da zai fi tunawa da su sun hada da Ali, Garba, Nwakocha da kuma John.
Ana wata sai ga wata, don wani azzalumin malami sai ya rika karbar kudi gun mahaifinsa, don ya tallafa masa ya ci jarawawar zuwa sakandare. Amma Salisu ya ce wa mahaifin nasa ya daina bayar da kudin, don shi ya san yana kokari don zai iya cin jarabawan. Amma mahaifinsa ya biris da shi.
Bayan Salisu ya ci jarabawa sai aka tura shi Kwalejin Tunawa da Sardauna da ke Kaduna (SMC), inda ya yi karatu har ya idar a 1982. Kafin ya kammala karatu a shekarar 1988, Shugaban makarantar Alhaji Haruna dalhatu, wanda dalibai suka lakaba wa suna ‘mugu’ don yana horar da dalibai da su yi karatu, yana yi musu fada yana cewa: “Ku dage ku yi karatu yau, don ku ji dadi gobe, ku bar neman mata, ku yi karatu, in kun samu digiri, mata kyawawa ba munana ba za su so ku.” Salisu Bala ya ci jarabawar gama sakadandare ta SSCE a fannoni shida Turanci, Tarihi, Ilmin Addinin Musulunci, Bayoloji, Hausa da Jogirafi. Daga nan ya shiga Kwalejin Share Fagen Shiga Jami’a ta Zariya a 1989, inda ya karanta Tarihi, Larabci da Addinin Musulunci. Da y ci jarrabawa sai Farfesa Asma’u Garba ta tagaza masa ya sami gurbin karatun digiri a Jami’ar Bayero da ke Kano. Bayan ya yi watanni uku sai Jama’ar Ahmadu Bello ta ba shi gurbin karatu a fannin Shari’a, amma ya ci gaba a Kano.
Abin mamaki shi ne, yana karatu sai Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ta ba shi aiki, lokacin yana da shekara uku a jami’a, don ya fassara mata littattafan Larabci na magabata zuwa Turanci. Amma sai Salisu ya ce sai ya kammala karatu kafin ya fara aiki.
Abin la’akari shi ne, samun gurbin karatu daban sannan zaman makaranta daban. Salisu yana yin tattaki na tsawon kilomita goma daga jami’a a kan hanyar Gwarzo zuwa unguwar Kabuga don ziyartar kawunsa don neman na sa wa a bakin salati, sannan ya kwana a garejin mota don gidan ya yi wa kawunsa kadan da iyalansa da mahaifiyarsa. Wani lokaci kuma sai ya nufi kauyensu Gulu da ke karkashin karamar Hukumar Rimin Gado don ya samo kayan abinci da na masarufi. Ana mazuru ana shaho, Salisu ya samu digirinsa na farko.
Maigidan mahaifin Salisu Bala kuma tsohon Daraktan Gidan Sardauna, Farfesa Abdullahi Mahdi wanda ya rike hannun Salisu ya kai shi dakin karatu ya ba da umurnin cewa: “Ku bar wannan yaron ya yi amfani da littattafai duk da yake ba mai karatun digiri na biyu ba ne.”
Bayan ya yi hidimar kasa (NYSC) a kwalejin GSS Maiduguri sai ya yi koyarwa a makarantu masu zaman kansu, watau Yarmouk da kuma M.S.O. a Kaduna sannan ya samu aiki da Kwalejin Ilmi ta Jama’atu Nasril Islam da ke Unguwar Sarki. A nan sai likkafa ta yi gaba, inda aka ba shi aiki a Arewa House Kaduna a shekarar 2007. Da ya karbo takardar daukar aikin sai ya sami mahaifinsa ya nuna masa. Watau Salisu da mahaifinsa suna aiki wuri guda ke nan a Gidan Sardauna. Jibril Haruna (Zariya) ya fi dansa murna, don dansa ya wuce shi a gun aiki. Wannan bai hana Salisu fitowa daga ofis a kullum ba don ya je gun mahaifinsa ya tambaye shi ko za a aike shi, ko ya yi masa sayayya ko wata hidimi. Bayan shekara biyu sai dattijo Jibril Haruna ya yi murabus.
Bugu da kari Salisu mutum ne mai gyaran fuska sumul ba gemu ba gashin baki, don haka sabbin dalibai ke hada kafa da shi a cikin makaranta, amma duk lokacin da ya shiga aji don fara koyar da dalibai a kashin farko, sai su yi ta mamaki ganin kusan sa’ansu ya zama malami, musamman ma mai matsayin digirin-digirgir dan sheakaru 39. Kafin nan ya sami tallafi zuwa nazari na watanni uku zuwa kasar Afirika ta Kudu daga wata cibiya mai suna ACLS a Amurka.
Wani abin ta’ajibi shi ne, lokacin da ya kammala digirinsa na biyu sai ya yi kicibis da tsohon malaminsa na makarantar firamare mai suna Malam Garba, wanda yake aikin leburanci na yin fenti, sai malamin ya ce kudin sallama daga aiki bai fito ba, shi ya sa ya koma aiki fenti.
Bugu da kari, yayan Bala wanda suka yi firamare tare yana shirin komawa jami’a don yin karatun digiri na biyu.