✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kyautar Dala 5000 daga Gwamna ta yi awon gaba da ma’aikatan Muryar Amurka

Lokacin da wakilan Gwamnan Jihar Kano Aminu Masari ya ziyarci sashin Hausa na Rediyon Muryar Amurka (BOA) da ke birnin Washington DC a ranar 9…

Lokacin da wakilan Gwamnan Jihar Kano Aminu Masari ya ziyarci sashin Hausa na Rediyon Muryar Amurka (BOA) da ke birnin Washington DC a ranar 9 ga watan Janairun , 2018, babu daya daga cikin fiye da ma’aikata 15 da ya yi tsammanin cewa ziyarar ta Gwamnan ta kunshin wata matsala da za ta iya jawo a kore su daga aiki.

An gudanar da tattaunawa kuma an zagaya da ayarin Gwamnan sassan ofishin gidan rediyon. Kuma a lokacin da Gwamnan ya shiga motarsa daya daga cikin manyan jami’an Gwamnatin Jihar Katsina da ke cikin ayarin ya mika “ambulan mai rawaya” dauke da Dala 5000 ga daya daga cikin ma’aikatan BOA din da ya bi su zuwa motarsu.

Sai dai Kakakin Gwama Masari, Malam Abdu Labaran ya musanta cewa maigidansa ne ya bayar da wani kudi ga ma’aikatan Muryar Amurka a lokacin ziyarar.

Sai dai majiyoyi da dama sun shaida wa Aminiya cewa ‘Gwamnan Arewa maso Yamma’ da Muryar Amurka ya ambata shi ne Gwamnan Jihar Katsina.

“Kyautar ta Gwamnan” daga baya an rarraba ta a tsakanin dukan ma’aikatan Sashin Hausar da suke aiki a wancan lokaci. Kuma kowa ya koma bakin aiki. Wadansu daga cikin wadanda suka ci gajiyar kyautar sun hada da Sahabo Imam Aliyu da Jummai Ali da Ladan Ayawa da Ibrahim Jarmai da Abdoul’aziz Adili Toro da Ibrahim Alfa Ahmed da sauransu.

Da farko dai babu wata alamar matsala kan ‘kyautar’ Gwamnan har sai dai Shugaban Sashin Hausa wanda yake hutu a Najeriya a lokacin ya koma aiki, kuma ya yanke shawarar ya zama mai fallasawa.

Mista Leo Kean ya rubuta takardar koke ga mahukuntan Muryar Amurka kan “bayar da kudi ba bisa ka’ida ba na Gwamnan” ga abokan aikinsa.

Dokar Tarayya ta Amurka ta haramta wa ma’aikatan Muryar Amurka karbar kyautar kudin da suka haura Dala 20 a lokacin da suke aiki.

Daga nan sai aka kaddamar da bincike kan “kyautar” Kuma a ranar 2 ga Oktoban bana, sai Muryar Amurka ya bayar da sanarwar kora ko shirin sallamar ma’aikatansa 15 na Sashin Hausa bayan da bincike ya gano a daidaikunsu sun karbi kudi ba bisa ka’ida ba daga wani jami’i daga Afirka ta Yamma.

Daraktar Muryar Amurka, Amanda Bennett, ta shaida wa ma’aikatan gidan rediyon da gwamnatin Amurka ke daukar nauyinsa kan matakin ta hanyar sakon imel din gidan rediyon.

“Don haka cike da bakin ciki, ina shaida muku cewa mun salami ko (kamar yadda dokokin Tarayya da ka’idoj) shirin sallamar ma’aikatan Sashin Hausa 15,” ta rubuta.

Daraktar ta ce daukar matakin ya biyo bayan cikakken binciken ma’aikatan Sashin Hausa da Ofishin Sufeto Janar na ’Yan sanda kan kan “Zargin aikata ba daidai daga ma’aikatan sashin, wanda ya kunshi karbar kudi ta haramtacciyar hanya daga wani jami’i a yankin da suke aiki.”

Sashin Hausa na Muryar Amurka yana da masu sauraro miliyan 20 a kowane mako, kuma an kafa shi ne domin al’ummar Najeriya, amma yana hadawa da Nijar da Ghana da Kamaru da kuma Chadi.

Ma’aikatan 15 da lamarin ya shafa, sun hada da Mista Kean (wanda ba ya cikin wadanda suka karbi kudin), sun hallara a kofar shiga hedkwatar Muryar Amurka daga washegari inda aka kwace ’yancinsu na shiga ginin kuma aka ba su wasikun da ke sanar da su matakin da aka dauka.

Rahotanni sun ce binciken da aka gudanar ya nuna ba a samu wata hujja da ta nuna kyautar ta yi tasiri ga wani shiri na gidan rediyon ba.

Sannan binciken Aminiya ya gano cewa Mista Kean ya samu kansa a cikin matsala ce bisa zargin aikata “wadansu harkokin badakalar kudade.”

Wasu daga cikin “laifuffukansa” sun hada da cushe a cikin kudin biyan hayar ofishin sashin na Abuja da yanke albashin ma’aikatan wucin-gadi da biyan albashi ga ma’aikatan bogi da sauransu.

Bayanai sun ce, masu bincike daga Hukumar Bincike ta Tarayya (FBI) sun zo Najeriya don bincikar cushen kudin hayar ofishin. Kuma sun yi magana da ma’aikatan wucin-gadi da dama da Mista Kean ya dauka aiki, kuma ya tilasta su su rika tura masa wani yanki mai kauri na kudin da ake biyansu a wata-wata.

Wadansu daga cikin ma’aikatan ma Rediyon Muryar Amurka ya dauke su a jirgi zuwa Washington DC domin su bayar da shaida a gaban masu bincike kan lamarin. Wata majiyar ta shaida wa Aminiya cewa, a baya wadansu ’yan jaridar Muryar Amurka an kore su daga aiki “saboda yin amfani da tarho din ofishin don kira na kashin kansu.”

Sannan Bennett, ta fadi a sakon imel dinta cewa “an kaddamar da wani bincike domin gano ko an samu wani tasirin kyautar a kan wani shirin Muryar Amurka. Idan aka samu mudahana za mu dauki matakin da ya dace bisa gaskiya.”

‘Karbar ‘kyauta’ daga mutanen da ake hira da su ba halattace ba ne.’

Kuma Daraktan Sashin Afirka, Negussie Mengesha ya ce ma’aikatan Muryar Amurka “sun fahimci cewa ba a amince da haka ba balo-balo.”

Faruwar wannan lamari, yanzu an bar sashin da ma’aikatan gwamnati na dindindin 11 kacal da ’yan kwantaragi su rika gudanar da shirye-shiryen rediyo na awa 16 da kuma minti 30 na shirin talabijin duk mako.

Daraktan Afirkar ya ce kafar labaran za ta ci gaba da gudanar da shirye-shiryenta da take gudanarwa a yanzu tare da taimakon wani dimbin masu aikin wucin-gadi da suke tallafawa daga Afirka. Kuma Muryar Amurka ya bayar da sanarwar cewa tsohon Shugaban Sashin Hausa, Fred Cooper, zai dawo ya ci gaba da gudanar da sashin har zuwa lokacin da za a zabi shugaban sashin na dindindin.

Mengesha, ya ce za a hanzarta maye gurbin ma’aikatan da aka sallama cikin gaggawa, kuma sababbin ma’aikatan za su samu cikakken horo kan aikin jarida.

Sai dai a fili yake cewa ba za a maye gurbin wadansu ma’aikatan ba a karkashin dokokin tarayya har sai an kammala bin doguwar hanyar da ake bi wajen sallamar ma’aikatan.

Bennett ta ce, “kowane mutum a wannan gini ya san dokokin tarayya da kuma ka’idojin aikin jarida. Kuma mutan za su gani (daga korar ta ranar Talata) cewa mun dauki wannan mataki da matukar muhimmanci. Kowa ya ga abin da muke fata daga gare su.”

Dabi’ar karbar na goro

Karbar kudi daga jami’an gwamnati da daidaikun mutane a Najeriya lokacin daukar labarai abu ne da ya zama ruwan dare duk da cewa doka ba ta amince ba.

Majiyoyin da suke da alaka da batun sun ce kusan daukaci “jami’an gwamnati daga Najeriya da suka ziyarci Muryar Amurka sun bayar da kudi bayan ganawarsu. Wannan ita ce al’adar. Kuma wannan ba yana nufin ’yan jaridar ne suke neman a ba su ba. Gaskiyar maganar ita ce: jami’ai ne kan bayar da kudin su kuma ’yan jaridar su karba,” inji majiyar wadda ba ta so a ambaci sunanta.

Masari bai bayar da kudi ga ma’akatan Muryar Amurka ba- Mukarrabinsa

Babban Mai tallafawa ta Musamman ga Gwamna Masari, Malam Abdu Labaran, ya musanta cewa maigidansa ne ya bayar da kudin da ya jawo korar ma’aikatan 15.

“A saninmu ba Gwamna Masari ba ne, saboda babu daya daga cikin wadanda abin ya shafa da ya ambaci cewa Gwamna Masari  ya ba su kudi, wannan shi ne matsayina. Ba zai zamo Gwamna Masari ba, domin ikirari ne daga bakinsu. Sun ce wani Gwamna daga Arewa maso Yamma, don haka tana iya yiwuwa kowanne daga cikin su gwamnoni bakwai na Arewa maso Yamma. Wannan ne matsayina. Hakika babu wanda ya ambaci Masari,” inji Labaran.

Sai dai Kakakin Gwamnan ya tabbatar da cewa Masari ya je Amurka a baya-bayan nan. “Gwamna ya ce Amurka a lokuta da dama a sanina. Kuma ba zan iya tuno aukuwar irin wannan lamari ba. Har sai in wani ya fito daga cikinsu ya ce Masari ne ya bayar da kudin hakan zai tabbata, idan ba haka ba, matsayina a fili yake cewa ba shi ba ne,” inji shi.

Duk kokarin da Aminiya ta yi domin jin ta bakin wadansu daga cikin ma’aikatan da aka kora ya ci tura, inda ta kira wayoyin wadansu daga cikinsu, amma ba su dauka ba, sannan ba su maido da sakon tes ko na whatsApp da aka aike musu ba. Su ma ma’aikatan wucin-gadin da suka yi korafin Mista Kean ya rika tatsar albashinsu sun ki amsa kiran wayar da Aminiya ta yi musu don neman karin bayani, haka ba su mayar da sakon da ta aike musu ba.