Gwamnatin tarayya na shirin bude makarantu domin ci gaba harkokin neman ilimi a fadin Najeriya.
Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ya ce nan gaba kadan gwamnatin za ta fitar da tsarin bude makarantu ba tare da yaduwar cutar ba.
Boss Mustapha ya ce Ma’aikatar Ilimi da kwamitin fadar shugaban kasa na duba hanyoyin bude makarantun cikin aminci.
A jawabinsa kwamitin na ranar Laraba, Boss Mustapha ya ba da tababacin yin iya kokarin domin na ci gaba da karatu yanda ya dace.
- Hotuna: Ranar yara ta duniya
- El-Rufai ya sauya dokar kullen coronavirus
- COVID-19 An sake rufe wasu kananan hukumomin Katsina
Boss Mustapha wanda ke jagorantar kwamitin ya ce rufe makarantu domin dakile yaduwar cutar coronavirus shi ne abin da ya fi dacewa.
Sai dai ya kuma matakin ya kara tsananta matsalar yawan yaran marasa zuwa makaranta tun kafin bullar annobar COVID-19.
“Muna kiran jihohi da kanana hukumomi da masu makarantu su fara tattauna hanyoyin sake bude makarantu,” inji shi.
Ya ce “kungiyar masu makarantu na neman gwamnati ta ba su rance mara ruwa da za su biya bayan an daga musu kafa na shekaru biyar.
Kafin su kungiyar masu makarantu ta kasa ta roki gwamnatin ta tallafa musu domin rage tasirin COVID-19 a kan harkokinsu.