✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda gobara ta lakume rayuka 11 da gidaje a Kano a wata guda

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce samu kiran gaggawa 55 a cikin watan Agusta.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta ce mutane 11 ne suka mutu da kuma gidaje da suka kone sakamakon gobara da aka samu a watan Agusta.

Kakakin hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ya bayyana cewa hukumar ta samu kiran gaggawa guda 55 a a cikin watan na Agusta.

Alhaji Saminu Abdullahi ya ce hukumar ta samu nasarar nasarar ceto rayukan mutum 91 da gidajen da darajarsu ta kai Naira miliyan 24.9, a wurare 29 da gobara ta tashi a tsawon lokacin.

“Mun samu kashe gobara kafin ta yi gagarumar barna a gidajen da jimillar darajarsu ta kai N24.9 duk dai a watan na Agusta,” in ji shi.

Jami’in ya kuma bayyana cewa sun samu kiran waya na karya guda 14 kan tashin gobara a cikin watan da ya kare.

Don haka ya ce akwai bukatar al’umma su rika kiyayewa wajen amfani da wuta don gudun haddasa tashin gobara.

Haka kuma ya bukaci masu ababen hawa su rika tuki da kulawa, domin rage aukuwar hadurra a kan hanya, musammn ma a wannan lokaci na damina.

%d bloggers like this: