✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gayyatar da Majalisa ta yi wa Alkalin Alkalan Kano ta tada kura

Gayyatar dai ba ta rasa nasaba da hukuncin da wata kotu ta yanke a kwanan nan.

Wata takardar gayyata da Majlisar Dokokin Jihar Kano ta aike wa da Alkalin-alkala Jihar, Mai Shari’a Nura Sagir Umar kan ya bayyana a gabanta na ci gaba da tayar da kura a Jihar.

Bayanai sun nuna cewa takardar wacce ke dauke da sa hannu Daraktan Harkokin Shari’a na majalisar, Nasiru Aliyu dauke da kwanan watan 26 ga watan Yulin 2021, ta umarci Alkalin-alkalan da ya bayyana a gaban kwamitin ranar 28 ga watan Yuli.

Rahotanni sun ce gayyatar ba za ta rasa nasaba da wani hukuncin kotu da Mai Shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya yi a kwanakin baya ba, inda ya dakatar da Majalisar daga ci gaba da tuhumar dakataccen Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Cin hanci da Rashawa ta Jihar, Muhuyi Magaji Rimingado.

Sai dai rahotanni sun ce Alkalin-alkalan ya yi biris da gayyatar inda ya ki zuwa sannan ya ki ya rubuta musu amsa.

Kakakin bangaren Shari’a na Kano, Baba Jibo Ibrahim ya shaida wa wakilinmu cewa sun yanke shawarwar kai batun gaban shugaban Kungiyar Lauyoyi ta Kasa (NBA) reshan jiyar Kano, saboda kaucewa ka-ce-na-ce tsakaninsu da majalisar.

Lamarin ya bamu mamaki – NBA

Da wakilinmu ya tuntubi shugaban NBA na Jihar Kano, Aminu Gadanya, ya ce Alkalin-alkalan yayi daidai da ya ki amsa gayyatar majalisar.

Ya ce, “Gaskiya abin ya zo mana da ba-zata. Na kadu matuka da na ji wai kwamitin Majalisar Kano na sammacin Alkalin-alkalai.”

Ya ce idan ma Majalisar ba ta gamsu da wani hukuncin kotu ba ne, kamata ya yi ta daukaka kara ko ta bukaci wata kotun ta sauya hukuncin.

“Ba daidai ba ne su gayyaci Alkalin-alkalai. Ko da Alkalin da ya yanke hukuncin ba su da hurumin gayyatarshi, ballantana Alkalin-alkalai gaba daya. Ba ma goyon bayan hakan kwata-kwata. Mun ma yi matukar mamakin ganin wai dan kungiyarmu ne ya rattaba hannu a kan takardar gayyatar,” inji Gadanya.

Da aka tambaye shi ko kungiyar za ta dauki wani mataki a kan lamarin, sai shugaban ya ce idan suka sami korafi, za su duba su ga ko hakan ya saba da ka’idojin aikinsu, ko kuma a’a.