Hukumar Yaki da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), ta yi awon gaba da Farfesa Hafsat, matar Gwama Ganduje na Jihar Kano, zuwa ofishinta domin amsa tambayoyi kan zargin rashawa.
Jami’an EFCC sun yi wa matar gwamnan takakkiya ne har zuwa Kano suka tisa keyarta zuwa hediwatar hukumar da ke Abuja inda ta amsa tambayoyi kan rashawa da danta Abdulazeez ke zargin ta da aikatawa.
- A kwace shagunan magoya bayan IPOB —Matasan Arewa
- ’Yan Boko Haram na tilasta aurar da kananan yara a Neja
Yunkurin Aminiya na magana da kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya ci tura, amma wani babban jami’in hukumar ya tabbatar maan cewa jami’an hukumar sun tafi da mai dakin gwamnan ne saboda ta ki amsa gayyatar a hukumar ta yi mata kan zargin da ake mata.
Farfesa Hafsat, wadda aka fi sani da Gwaggo ta shafe daren Litinin a ofishin EFCC, inda aka yi mata ruwan tambayoyi kan tuhumar da tafe fuskanta.
Hakan ta faru ne bayan matar gwamnan ta yi biris da goron gayyatar hukumar, kan karar da dan Gwaggo, Abdulazeez Ganduje, ya kai wa hukumar, yana zargin ta da almundhana da badakalar filaye.
Wata majiya mai tushe a Gidan Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar wa Sashen Hausa na BBC da hakan, amma ta ce hukumar ta riga ta sako matar gwamnan.
A safiyar Talata ce dai Gwaggo ta koma Kano, bisa rakiyar Gwamna Ganduje, kamar yadda aka ga hadimin gwamnan, Abubakar Aminu Ibrahim, ya wallafa hotunan dawowar tasu.
A hotunan an ga Gwamnan Abudullahi Ganduje tare da matar tasa suna saukowa daga jirgin sama a Filin Jirgi na Malam Aminu Kano da ke Kano.
Sai dai kuma Kwamishinan Yada Labaran Jihar Kano, Muhammad Garba, ya ce babu kamshin gaskiya a maganar tsare matar gwamnan da ake rade-radin hukumar ta yi.
A cewarsa, Farfesa Hafsat tana nan tana ci gaba da gudanar da harkokinta a matsayin mai dakin gwamnan jihar.
Don haka ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar.