✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dan Boko Haram ya shiga hannu

Wani dan Boko Haram dan shekara 20 ya shiga hannu a Jihar Ondo bayan wasu kwanaki da ya yi ikrarin kashe mutane biyu a wata…

Wani dan Boko Haram dan shekara 20 ya shiga hannu a Jihar Ondo bayan wasu kwanaki da ya yi ikrarin kashe mutane biyu a wata gona da ke jihar, tun bayan da mahaifinsa ya koro shi daga Kano.

Mutumin mai suna Bashir Mohammed wanda aka nuna shi a hedkwatar ‘yan sanda ta Jihar Ondo, ya bayyana wa Aminiya cewa kisa ba wata matsala ba ce a gare shi.

Mutumin da ake zargi da aikat alaifukan dan asalin Jihar Nasarawa ne, wand aya ce mahaifinsa ne ya koro shi daga gidansu da ke Kano saboda hankalin mahaifinsa bai kwanta da yadda ke gudanar harkokinsa ba, don haka ya yanke wwsa kansa tafiya kudu har ta kai ga ya karke da shiga komar ‘’yan sanda.

Basir ya ce shi da sauran ’yan kungiyarsu ta Boko Haram suna aiki ne tare da wasu manyan mutane, wadanda ke kiransu su hadu a daji su tattauna kan yadda za su aiwatar da ayyukansu a wasu wurare.

“Suna ba mu bindigogi, sai mu tafi duk inda suka umarce mu,” inji shi.

Lokacin da ake nuna wanda ake zargin, Kwamishinan ’yan sandna jihar Gbenga Adeyanju ya gaya wa manema labarai cewa an kama Bashir ne kwanaki uku da suka gabata a karamar Hukumar Isua-Akoko ta Ku8du maso Gabas bayan da suka samu bayanan sirri.

Adeyanju ya tuna da cewa a daidai wannan wuri suka taba kama wani Kwamandan kungiyar, Idris Ibrahim Babawo mai lakabin Idoko a makonnin da suka wuce.