✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bindigogin sirri ke barazana ga Afghanistan

Jami’an tsaro a Afghanistan sun kama tulin bindigogi masu siffar alkalami da suke zargin ’yan ta’adda da sauran miyagu na amfani da su a yayin…

Jami’an tsaro a Afghanistan sun kama tulin bindigogi masu siffar alkalami da suke zargin ’yan ta’adda da sauran miyagu na amfani da su a yayin da kasar ke fama da kashe-kashen siyasa.

’Yan sanda a birnin Kabul — hedikwatar kasar — mai fama da kashe-kashen siyasa sun ce bindigogin masu daukar harsashi daya-daya ne kuma sunana da wuyar ganewa.

“Bindigogin na da siffar biron da ake dannawa idan za a yi rubutu ta yadda idan mai maharbi ya sa harsashi a ciki zai saita abin da zai harba sannan ya dannan maballin da ke zama a matsayin kunamar bindigar”, inji wani jami’in Sashen Binciken Manyan Laifuka (CID) a Kabul.

A karshen makon jiya ne ’yan sanda suka bankado bindigogi masu siffar alkalami guda 48 a cikin tarin wasu makamai da aka kama da suka hada da bom na likawa a jikin wurare, da ake tayarwar daga nesa.

Kakakin Ma’aikatar Tsaron Afghanistan, Tariq Arian ya ce, “’yan ta’addan na so su yi amfani da makaman ne wurin yin kashe-kashe a Kabul”.

  • Tabarbarwar tsaro a Kabul

Karuwar rashin aikin yi da fatara sun kara tsananta matsalar tsaro a birnin mai fama da masu garkuwa da mutane da fashi da kuma harbe-harbe barkatai.

Matsalar ta kara tsanani bayan kashe-kashen siyasa da ake yi wa masu fafutikar zaman lafiya da masana da kuma jami’an gwamanti.

“An kashe akalla mutum 40 a irin wadannan hare-hare a Kabul kadai cikin watanni shidan da suka gabata”, inji jami’in na CID.

Ya ce an yi ta kai hare-haren ne ta hanyar makaman da ba a kai ga ganewa ba, amma jami’an tsaro na kyautata zaton bindigogi masu fasalin abin rubutu ne.

  • Shin Taliban na da hannu?

Hukumomin kasar na zargin kungiyar Taliban da kungiyoyi masu alaka da ita da kai hare-haren.

Taliban wadda ta shiga yarjejeniya da Amurka a watan Fabrairu bisa sharadin ba za ta rika kai hare-hare ba ta nesanta kanta da hare-haren.

Sai dai hare-haren masu tayar da kayar bayan na ta karuwa a kan jam’ian tsaro a yankunan karkara, yayin da Taliban da gwamnatin Afghanistan ke kan tattaunawa a birnin Doha da Daular Larabawa domin kawo karshen yakin shekara 19 da bangarorin ke yi.