✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin tunawa da Fela na bana ya wakana

A makon nan ne aka gabatar da bukukuwa domin tunawa da mutuwar shahararren mawaki Fela Kuti bayan ya cika shekara 20 da mutuwa. Shi dai…

A makon nan ne aka gabatar da bukukuwa domin tunawa da mutuwar shahararren mawaki Fela Kuti bayan ya cika shekara 20 da mutuwa.

Shi dai wannan biki wanda ake kira Felabaration yana gudana ne duk shekara tun bayan da diyar mawakin Yeni Anikulapo Kuti ta fara shirya na farko a shekarar 1998 a Jihar Legas, inda mawaka da dama ke zuwa su baje kolin fasaharsu.

Shi dai Fela, an haife shi ne a ranar 15 ga watan Oktoban shekarar 1938 a garin Abeokuta da ke Jihar Ogun. Sannan kuma ya shahara ne a bangaren wakokin fafutukar kare hakkin dan Adam da kidan Afrobeat.

Daga cikin mawakan da suka baje kolinsu a ranar bikin akwai ‘ya’yan mawakin, Seun Kuti da Femi Kuti. Sai sauran mawaka irin su: Reminisce, Solid Star, Small Doctor, Terry Akpala, Terry G, Sound Sultan, Eba, Mz Kiss da sauransu.

A lokacin bikin, wasu daga cikin mawakan, kamar su Terry G da Small Doctor, sun rika jefa wa ’yan kallo kudi domin girmamawa ga mamacin mawakin.

Gwamnan Jihar Legas ya karrama Fela da mutum-mutumi

A wani bangaren kuma, Gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode ya karrama mamacin ta hanyar gabatar da mutum-mutuminsa a lokacin da ake bikin na Felabaration na bana.

Shi dai wannan mutum-mutumin an gabatar da shi a shatatalen Allen da ke Ikeja.

A cewar gwamnan “Mun hada wannan mutum-mutumin ne domin tunawa da Fela, da kuma tunawa da yadda ya rika fafutukar nema wa mutane ’yanci,” inji gwamna Ambode.

Gwamnan ya kara da cewa “Fela mutum ne da ya yi watsi da rayuwar jin dadi, duk da cewa mutum ne da ya gaji arziki, kawai domin ya ga mutane sun samu shugabanci mai kyau, kuma su san hakkin su. Wannan mutum ai ya cancanci a rika tunawa da shi,” inji Ambode.

Shi dai Fela ya rasu ne a ranar 2 ga watan Agustan shekarar 1997. Ya rasu yana dan shekara 58 a rayuwa bayan ya yi fama da ciwon zuciya. Sannan kuma ya bar ’ya’ya bakwai. ’Ya’yan su ne Femi Kuti, Seun Kuti, Yeni Kuti, Sola Kuti, Omosalewa Anikulapo Kuti, Kunle Anikulapo Kuti, Motunrayo Anikulapo Kuti.

Mawakin dai ya sha samun matsala da shugagabannin kasa a lokacin yana raye. Daga cikin shugabannin da ya samu matsala da su akwai Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari a lokacin suna mulkin soja. Sannan kuma ya taba kwashe wata 20 a gidan yari a lokacin mulkin Buhari na soja, wanda shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida ya sake shi daga baya.

Daga cikin wakokin da suka jawo masa matsala da shugabanni akwai Zombie da I.T.T. (International Thief-Thief).