✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin sulhun P-Square ya wakana ranar Kirsimeti

Mawakan dai sun bata ne tun shekarar 2016, ba sa tare da juna.

A ranar bikin Kirsimeti ce fitattun ’yan biyun mawakan nan, Peter da Paul, da aka fi sani da P-Square suka shirya gagarumin biki domin nunawa duniya sun sulhunta kansu.

’Yan biyun dai sun hade ne bayan sun shekara biyar a rabe suna gudanar da harkokinsu.

A watan Nuwamba ne suka sanar da sulhun a wani faifan bidiyo da suka fitar sun rungume juna a wani daki, yayinda wasu a gefe suka rika tafawa.

Haka nan kuma manajansu, wanda shi ne babban yayansu, Jude Okoye shi ma yana cikin dakin.

An dade ana ta kokarin sulhunta mawakan ’yan uwan juna tun rabuwarsu a shekarar 2016, amma abin ya ci tura.

Daga cikin abubuwan da suka kawo musu matsala akwai matsayin yayansu Jude da kuma auren Paul da budurwarsa, Anita.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin sulhun akwai Tony Elumelu, Kate Henshaw, Linda Ikeji, Jude Okoye, Lola Omotayo da sauransu.

Wani karin arashi na bikin shi ne yadda ’yan biyun suka shirya tsakanin wasu abokan guda biyu, wato Timaya da J. Martins da su ma suka yi shekara kusan bakwai suna rikici.

Mawakan sun yi waka tare a bikin, a wani irin abu da masoyansu suka dade suna sha’awar sake gani.

A taron, sun rera wakokinsu na ‘Chop my money’ da ‘Ifunaya’ da sauransu.

A tsakiyar bikin ne Mr P. ya tsayar da komai, ya ce suna neman afuwar masoyansu bisa kuskuren da suka yi na rabewa, sannan ya umarci kaninsa suka tsuguna tare suna ba masu kallon hauri, sannan a karshe aka sa wakar ‘Alingo’ inda a ciki ake cewa ‘P-Square is back again’ sannan babban abokinsu May D ya fito inda suka yi wakar nan da suka yi a tare ta ‘Chop my money’.

Daga cikin fitattun wakokin ’yan biyun akwai ‘Chop my money’ da ‘Ifunaya’ da ‘Alingo’ da ‘Personally’ wanda ake irin rawar Michael Jackson da ‘Do me’ da ‘Testimony’ da ‘Bizy body’ da sauransu.

Bikin sulhun wanda suka sa wa suna ‘P-Square reunion concert’ ya samu halartar manyan baki daga cikin mawaka da ’yan siyasa da ’yan kasuwa na kasar nan.