✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin kona gawar Shashi Kapoor ya gudana cikin girmamawa

A ranar Talata da ta gabata ne aka gudanar da bikin kona gawar shahararren dan wasan masana’antar Bollywood na Indiya Shashi Kapoor a wajen kona…

A ranar Talata da ta gabata ne aka gudanar da bikin kona gawar shahararren dan wasan masana’antar Bollywood na Indiya Shashi Kapoor a wajen kona gawa na Santacruz Hindu kamar yadda al’adar addinin Hindu ya tanadar.

Tsohon dan wasan ya mutu yana da shekara 79 a Asibitin Kokilaben Dhirubhai na birnin Munabi bayan ya yi fama da matsananciyar jinya na dogon lokaci.

Gwamnati ne ta dauki nauyin gudanar da bikin domin girmamwa ga tsohon dan wasan. Inda ‘yan sanda suka dauko gawar lullube da tutar kasar, sannan suka ciro gawar aka konata bayan an yi shiru na minti daya domin girmamawa ga tsohon dan wasan wanda ya yi sama da shekara 40 a masana’antar ta Bolluwood.

‘ya’yansa guda uku: Kunal, Karan da Sanjna ne suka jagoranci kona gawar tare da sauran ‘yan uwa da abokanan arzikin iyalan gidan Kapoor din.

Sakonnin ta’aziya ga mamacin a shafuka sada zumunta a cikin kasar Indiya da ma duniya baki daya.

Shi dai Shashi Kapoor, an haifeshi ne a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 1938, a garin West Bengan na na Gabashin Indiya. Sannan kuma ya fara yin fim ne a shekarar 1961, inda ya fito a babban dan wasan a wani fim mai suna Dharamputra. Duk da cewa rahotanni na nuna cewa ya fara yin fim tun yana karama tun a shekarun 1940s.

Rahotanni na nuna cewa mamacin ya yi finafinai sama da 175, yawanci na Bollywood, da kuma wasu na turancin Ingilishi day a fito. Kuma ya samu kyaututtuka da dama a lokacin rayuwarsa.

Daga cikin finafinansa da suka shahara akwai Deewar, Saryam Shiban Sundran, Junoon, Shaan, Namak Halaal da dai sauransu.

Manyan ‘yan finafinan Indiya sun halarci taron, daga cikinsu akwai Amitabh Bachchan, Aishwarya Rai, Rani Mukerji, Sanjay Dutt, Abhishek Bachchan, Saif Ali Khan da Shah Rukh Khan da dai sauransu.