✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Yadda barawon kananan yara ya fada komar ’yan sanda 

Ya ce ya saba sato kananan yana sayarwa N80,000

Wani mutum mai kimanin shekaru 35 ya fada komar ’yan sanda bayan ya sace wata yarinya mai shekara daya a kauyen Atolashe da ke Karamar Hukumar Odeda a Jihar Ogun.

Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi, ya bayyana cewa a ranar Larabar 23/02/22 ne dubun wanda ake zargin ta cika bayan da ya faki idon mahaifiyar yarinyar da ke toya garin rogo tana mai da shi garin kwaki ya dauke yarinyar ya yi yunkurin tserewa da ita.

“Dubunsa ta cika ne a lokacin da wani mutum ya lura da yadda yake sanda a lokacin da ya dauki yarinyar ya tafi da ita.

“Nan da nan mutumin ya ankarar da mahaifiyar yarinyar, inda aka sanar wa ’yan sanda da wasu mafarauta suka bi sawu suka kama shi a wani daji da ya labe, inda aka kwarbe yarinyar a hannunsa.

“A binciken da ’yan sanda suka yi masa ya shaida musu cewa a baya ya taba sato yara biyu a Jihar Legas da kuma yankin Akute na Jihar Ogun, inda ya sayar da su a kan kudi N80,000 ko wannensu.

“Ya ce akwai wasu mata biyu da idan ya sato yara yake kai musu su ba shi N80,000” inji DSP Abimbola Oyeyemi.

Oyeyemi ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Lanre Bankole, ya ba da umarnin kamo matan biyu cikin gaggawa domin zurfafa bincike tare da gabatar da su a kotu.