✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ambaliya ta rusa gidan mutumin da ke rubutu da kafa

Magidancin mai suna Ahmadu Yakubu wanda aka haife shi da bukata ta musamman, ya rasa muhallainsa sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a jihar Jigawa,…

Magidancin mai suna Ahmadu Yakubu wanda aka haife shi da bukata ta musamman, ya rasa muhallainsa sakamakon ambaliyar ruwan da ta auku a jihar Jigawa, in da ta rusa gidaje da dama.

A watan Agusta ne dai Aminiya ta kawo muku tattaunawar bidiyo da magidancin, wanda ya ki yin bara domin ciyar da iyalinsa, inda ya zabi yin rubutu da kafarsa domin samin abin dogaro.

To sai dai ambaliyar da ta auku a jihar, ta sanya shi da iyalinsa sun koma gararamba a gari, sanadiyar rashin matsugunin da suka samu kansu a ciki.

“’Ya’yana na ta faman kuka tun bayan faruwar lamarin, saboda rashin makwanci.

Makwabta sun taimaka mana mun kwashe kayanmu bayan aukuwar ibtila’in, sai dai ina cikin mawuyacin hali kuma na rasa yadda zan yi.

Wadannan dai su ne hotunan yadda gidan na sa ya dawo: