✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda al’amuran ilimi suka tabarbare a Najeriya

Babu raba daya biyu, duk wanda ya kwana kuma ya tashi a kasar nan, ya san cewa tabbas harkokin ilimi sun tabarbare a wannan kasa…

Babu raba daya biyu, duk wanda ya kwana kuma ya tashi a kasar nan, ya san cewa tabbas harkokin ilimi sun tabarbare a wannan kasa tamu. Shin laifin wane ne da wace ce wajen haddasa tabarbarewar ilimin?
Idan muka koma baya can, kimanin shekaru 40 zuwa 50 da suka gabata, harkokin ilimi suna da kima da martaba a kasar nan. Za ka ga malaman makaranta, musamman a karkara suna koyar da dalibai a gindin bishiyoyi; za ka ga dalibai zaune bisa tabarmi ko kan duwatsu, amma duk da haka, kafin yaro ya gama firamare, za ka same shi cike da fasaha da hazaka. Za ka ga dalibi ya iya karatu da rubutu, ba da Hausa kadai ba, har ma da Turanci.
A wancan lokacin, malamin makaranta abin darajawa ne, abin karramawa ne. Ana saurarensa a kowace harka. A karkara, daga Maigari, babu wani mai kima a idon jama’a, daga Limami sai kuwa Hedimasta.
Haka kuma, a wancan lokacin, za ka ga dalibai suna da lababi da biyayya da cikakkar da’a. Za ka sami dalibai suna daraja iyayensu da malamansu da sauran duk wadanda suka cancanci a yi musu da’a. Ba za ka samu dalibai na shiga kungiyar asiri ba, ba su ma san wannan ba ko kadan. Kowace makaranta ka leka, za ka samu kayan aikin koyarwa isassu. Wato littattafai na karatu da na rubutu, ga dakunan karatu ga yanayi mai kyau don koyo da koyarwa.
A wancan lokaci, gwamnati na kula da malaman makaranta, ba su da matsalar albashi ko wani alawus. Ana biyan su sosai yadda ya kamata. Malamin makaranta a irin wancan lokaci, babban mutum ne shi.
A irin wannan lokaci, dalibi ko firamare ya kammala, ba zai rasa aikin yi ba, koda kuwa na wucin-gadi ne, kafin ya shiga sakandare. Idan kuwa ya kammala sakandare, aikin gwamnati sai wanda ya ga dama zai zaba.
A yau din nan, idan mutum ya duba yanayin malaman makaranta, ya duba yanayin dalibanmu da yanayin makarantun da ake koyarwa a cikinsu, ba sai ya kai ruwa rana ba, zai tabbatar da cewa lallai harkokin ilimi sun tabarbare, har ma ana ganin cewa idan ba an yi da gaske ba, babu yadda za a iya kawo gyara mai alfanu a cikin harkar.
Mu yi tattaki zuwa wata makarantar firamare da ke yankinmu ko karkararmu, nan za mu ga abin bakin ciki da takaici. Ni dai na shiga wani aji na wata firamare a garinmu, abin da na gani ya sosa mini rai, ya jirkita mini kwakwalwa. Me na gani? Rufin ajin, iska ta kware rabi, don haka idan ana ruwa, ajin komawa yake kamar wani dan karamin gulbi. Babu tebura da kujeri a cikinsa, dalibai a kasa suke zama domin daukar darasi. Ba wannan ba ma, da na kirga yawan daliban da ke cikin ajin, sai da na samu guda dari da goma sha biyar. Da na tambayi monitan ajin, ko su nawa ne a rijista? Sai ya ce mini sun haura dalibai 150, amma wasu sun daina zuwa makarantar.
Idan zan yi tambaya, wane malami ne zai iya koyarwa a irin wannan aji mai yawan dalibai haka? Wane dalibi ne zai iya fahimtar wani abu a irin wannan gwamutsitsi? Amsar da ka samu, ita ce za ta bayyana maka yadda ilimi ya tabarbare tun daga tushe!
Kila ka ce, ai ajin firamare na je ko? Na ba ka dama, ka tafi wata sakandaren gwamnati ka yi kallo. Babu wani bambanci tsakanin matsalar da muka samu a ajin nan da na sakandare. Kada mu manta, mu dai a jiharmu, tuni an kasha mafi yawan makarantun kwana na sakandare. dalibai maza da mata, yanzu karatun je-ka-dawo ake yi. Ba ma sakandare ba, hatta makarantun gaba da sakandare, kai hatta wasu azuzuwan na jami’o’in kasar nan, suna fama da matsalar rashin abubuwan zama da ma karancin azuzuwan. Akwai wata jami’a da na ga dalibai na makalewa a taga, suna daukar darasi. Wane irin ilimi za a samu a irin wannan yanayi? Lallai za ka iya ba da amsa da kanka!
Wata babbar matsala da ke kawo wa harkar ilimi cikas, ita ce ta rashin isassun kudin gudanarwa, domin kuwa duk makarantar da ka je, za ka iske matsaloli masu tarin yawa, wadanda kuma suka danganci kudi. Wani abin takaicin ma shi ne, duk da cewa akan dan cefana wani kason kudi ga ma’aikatun ilimi, amma su din ma, sai ka ga ba a ririta su ga dawainiyar ilimin, sai ka ga ana sace su, ana karkatar da su zuwa inda Allah kadai Ya sani. A irin wannan, sai ka ga littattafan da aka saya da kudin gwamnati, domin rabawa a makarantu, amma ana sayar da su a kasuwa. Shin laifin wane ne wannan?
Majalisar dinkin Duniya ta fitar da wani kuduri, inda ta ce, duk wata kasa da ke son ci gaba, to ta ware kashi 26 cikin 100 na jimillar kasafin kudinta, ta mika su ga harkar ilimi. Wani abin ban haushi, mu a Najeriya, sai ka ga ana ware kashin da ya gaza goma ma. Wannan kankanin adadin da aka ware ma, kamar yadda muka ambata a baya, wasu karkatattun jami’an gwamnati ke sace su. Ta yaya ilimi zai bunkasa ke nan a kasar nan?
Wani abu da yake kara dagula lissafi shi ne, har yanzu ba mu samu ’yancin kanmu ba, idan dai ana maganar yaren kasa. A kasar nan, har yanzu da harshen Turanci ake koya harkokin ilimi. Ke nan, dalibi sai ya fara koyon bakon yare, sanan zai fara fahimtar abin da ake koya masa a makaranta. kasashen da duk suka ci gaba, da yarukan kasarsu ake koya ilimi. Misali, kasar China da Jafan da sauransu, duk da yarukansu ake koya wa dalibai darasi, yaya ba za su fahimta ba? Dalili ke nan suke fahimtar darussan da ake koya musu. Mu kuwa fa?
Ga wata babbar matsala kuma da ta yi mana cacukwi, idan dai muna maganar tabarbarewar harkokin ilimi ne a kasar nan. Wannan kuwa shi ne, yadda aka bari harkokin ilimi ya koma kasuwanci. An samu yaduwar makarantun kudi. Ga su nan birjik, tun daga na rainon yara har zuwa jami’o’i masu zaman kansu. ’Ya’yan wa da wa ke karatu a irin wadannan makarantu kuma me ya sanya?
Kamar yadda muka fahimta, yadda aka mayar da harkar ilimi ta zama harkar kasuwanci, hakan ya taimaka wajen tabarbarewar ilimi a kasar nan. A yau, za ka ga ’ya’yan attajirai da ’ya’yan manyan ma’aikatan gwamnati, ba su zuwa makarantun gwamnati, sai dai ka gan su a zababbun makarantun kudi. Wasu shafaffu da mai ma, ba makarantun cikin gida suke halarta ba, ina, sai dai ka ga an kai su kasashen waje. Abin kunya, sai ga shi wai daliban Najeriya ne ke zuwa daukar karatu a jami’o’i da kwalejojin kasar Ghana. Ke nan, su makarantunsu sun inganta, alhali na Najeriya, “Giwar Afrika” sun tabarbare.
A halin yanzu, tun daga ’ya’yan Shugaban kasa da ’ya’yan Ministan Ilimi da ’ya’yan Kwamishinan Ilimi da ’ya’yan Kansilar Ma’aikatar Ilimi, duk ba za ka same su a makarantun Gwamnati ba. Wannan ya kara nuna irin yadda aka yi watsi da harkar ilimi a kasar nan. Idan har dan Ministan Ilimi ba zai halarci makarantar da mahaifinsa ke kula da ingancinta ba, to ta yaya makarantun kasar nan za su inganta?
Wata matsalar kuma da take kara dagula harkar ilimi a kasar nan, ita ce yadda ake wulakanta malaman makaranta. A yau, ba kamar shekarun baya ba, an wulakantar da malaman makaranta, ba a dauke su a bakin komai ba. A yau ba sai gobe ba, albashin kansila ya fi na Firansifal, shugaban makarantar sakandare. Albashin dan Majalisar Tarayya, ya fi na Farfesa mai koyarwa a jami’a. Yaushe za a ci gaba a wannan wulakantaccen yanayi?
Ga babbar tambaya, su wane ne ke da alhakin lalacewar ilimi a Najeriya. Amsar guda daya ce – shugabani. Su ne ummul haba’isin lalacewar ilimi a kasar nan. Mafi yawa daga shugabannin da muke da su a yau din nan, da kudin gwamnati aka yi musu hidima, suka samu ingantaccen ilmi, amma su a yanzu, maimakon su maida biki, sai suka zabi su banzatar da harkar ilimin. Sun yi haka ne ta yadda suke kwashe ’ya’yansu, suna mika su kasashen waje karatu. Sun yi haka ne domin kada ’ya’yan talakawa su ma su samu ilimi, su zama wani abu kamar su ko kamar ’ya’yansu.
Maimakon su gyara harkar ilimi, ’ya’yan kowa da kowa su samu ilimi, su waye, sai suka gwammace su banzatar da ’ya’yan talakawa. Dalilin ke nan suka maida ’ya’yan marasa galihu ’yan bangar siyasa, wadanda suke tanadar wa kwayoyin maye, ba don komai ba sai domin su kare muradunsu a lokacin siyasa. Dalili ke nan za ka ga cewa, a lokacin da ’ya’yan shugabanni ke cikin azuzuwa, a kasashen waje, a wannan lokacin ne kuma ’ya’yan talakawa ke yawo da adduna da gariyo, suna fadace-fadace da juna, suna karkashewa da lahanta juna, saboda kare ra’ayin irin wadancan shugabanni a siyasance. Allah wadaran naka ya lalace, wai rakumin dawa ya ga na gida.