A yau mun kawo maku yadda ake yin salak din kokumba da tumatir, wanda yin sa na da sauki kuma yawan cin sa na kara lafiya.
Kayan hadi:
- Kokumba
- Tumatir
- Albasa
- Tatasai
- Gyanyen parsley
- Man zaitun
- Ruwan kal (Vinegar)
- Gishiri
- Sugar
- Bakin barkono
Yadda ake hadi
- A yi amfani da gishiri a wanke tumatir, kokumba, albasa, tatasai da gyanyen parsley, sai a daureye sosai a sa kowanne a gwagwa ya tsane.
- A yayyanka kowanne daga cikinsu a ajiye a gefe guda.
- Sai a samu kwano mai zurfi a zuba su a ciki.
- A barbada bakin barkono, gishiri da sukari sai a juya.
- Sai a sa vinegar da man zaitun a sake guyawa sosai.
Shi kenan salad ya yi sai ci.
A ci dadi lafiya.