✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake yin Pizza

Assalamu alaikum jama’a da fatan kuna cikin koshin lafiya.  Yau filin namu ya kawo muku yadda hake hada pizza ne, fatan za a jaraba. Kayan…

Assalamu alaikum jama’a da fatan kuna cikin koshin lafiya. 

Yau filin namu ya kawo muku yadda hake hada pizza ne, fatan za a jaraba.

Yadda hadawa:

Da farko za a jika yis da ruwan dumi na kamar tsawon mintoci 10, sai a zuba gishiri da man zaitun a ciki.

Bayan haka sai a zuba fulawa a cikin ruwan yis din aka kwaba har sai ya yi tauri.

A rufe kwababbiyar fulawar a bari ta yi minti 30 ko har sai ta kumbura.

A juye fulawar a faranti sannan a sa cikin oven a gasa shi na minti biyar.

A dauko tumatir, tatasai da albasa da aka yanka su kanana da kuma kayan kanshi a barbada a kai.

Sai kuma a dauko tsokar naman kazar da aka yanka ta kanana  a zuzzuba a kai.

A yaryada mayonnaise a kai, sannan a rufe samansa da cheese sai a mayar da shi cikin oven a kara gasshi na ‘yan mintoci sannan a sauke.

Wannan shi ne yadda ake hada pizza a gida.

Za a iya cin pizza shi kadai ko a kuma a hada shi da shayi.