Assalamu alaikum jama’a da fatan kuna cikin koshin lafiya.
Yau filin namu ya kawo muku yadda hake hada pizza ne, fatan za a jaraba.
- Kayan hadi
- Fulawa
- Gishiri
- Yis
- Man zaitun
- Manshanun kanti (Cheese)
- Mayonnaise
- Kayan kamshi
- Tumatir, albasa da tattasai
- Tsokar kaza
- Yadda ake hada jus din karas cikin sauki
- Yadda ake miyar kuka da man shanu
Yadda hadawa:
Da farko za a jika yis da ruwan dumi na kamar tsawon mintoci 10, sai a zuba gishiri da man zaitun a ciki.
Bayan haka sai a zuba fulawa a cikin ruwan yis din aka kwaba har sai ya yi tauri.
A rufe kwababbiyar fulawar a bari ta yi minti 30 ko har sai ta kumbura.
A juye fulawar a faranti sannan a sa cikin oven a gasa shi na minti biyar.
A dauko tumatir, tatasai da albasa da aka yanka su kanana da kuma kayan kanshi a barbada a kai.
Sai kuma a dauko tsokar naman kazar da aka yanka ta kanana a zuzzuba a kai.
A yaryada mayonnaise a kai, sannan a rufe samansa da cheese sai a mayar da shi cikin oven a kara gasshi na ‘yan mintoci sannan a sauke.
Wannan shi ne yadda ake hada pizza a gida.
Za a iya cin pizza shi kadai ko a kuma a hada shi da shayi.