✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake yin jus din gurji

Wannan irin jus din na taimakawa wajen wanke duk maikon da aka ci bayan an sha ruwa.

Assalamu alaikum uwargida, yaya azumi? Da fatar ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin jus din Gurji domin buda baki.

Wannan irin jus din na taimakawa wajen wanke duk maikon da aka ci bayan an sha ruwa.

A sha ruwa lafiya.

Abubuwan da za a bukata

· Gurji

· Lemun tsami

· Citta

· Na’a’na’a shayi

· Sukari

· Jus din soda

Hadi

A wanke gurji sannan a yayyanka shi kanana, a matse ruwan lemun tsami da citta da kuma na’a’na’an shayi sai a markada su a bilinda.

Bayan an gama, sai a tace su a zuba sukari a gauraya har sai sukarin ya narke sannan a fasa kankara a zuba sai a gauraya.