Tsamiya na da anfani ga lafiyar dan Adam, ciki har da zamanta abin yin kayan sha na marmari.
Tsamiya na kara lafiyar hanta, kashi da zuciya, tana kuma wanke ciki, gyara fata, rage kiba da hawan jini da kuma kara lafiyar mata ta masu juna biyu.
- Yadda ake miyar kaza da dankalin turawa
- NAJERIYA A YAU: Yadda harkar Kudi ta intanet ta Sa ’yan Najeriya tafka asara
Shi ya sa yau muka kawo muku yadda ake yin ‘juice’ din tsamiya:
Kayan hadi
- Tsamiya
- Citta
- Lemo
- Suga
- Filebo
Yadda ake hadi
A wanke tsamiya a babbare a jika ta a ruwa.
2. A markada citta a tace sai a agije ruwan a gefe.
3. A markada jikakkiyar tsamiyar a tace, sai a ajiye.
4. A juye tattaccen ruwan citta da tsamiyar a babban mazubi.
5. Sai a matse ruwan lemuo a zuba a ciki.
6. A sa ‘flavour’ mai irin kamshin da ake bukata a ciki.
7. A zuba suga daidai yadda ake so sannan a juya hadin.
Shi ke nan sai a sa a firinji, ya yi sanyi a sha haka, ko kuma a sa kankara a ciki a sha.