Shekaru da dama bayan fitar rahotanni game da jan kafa kan shari’o’in kisan gilla da ba a kai ga warware su ba a Nijeriya, inda ta kai ga wasu masana suna bayyana wasu daga cikin shari’o’in ma kan mutu murus ba tare da ganin karshensu ba, tamkar yadda wadanda aka kashe suka mace ba tare da kaiwa ga karshen shari’ar ba.
Shari’o’in kisan gilla da ba a kai ga warware su ba a Nijeriya sun hada da na Dele Giwa da na James Bagauda Kalto da Olaitan Oyerinde da Bola Ige da Kudirat Abiola da Funsho Williams da Alfred Rewane da Marshal Harry da Aminosoari Kala Dikibo da Dipo Dina da Sunday Ugwu da kuma na Tordue Salem.
Dele Giwa
Dele Giwa tsohon Editan Mujallar Newswatch, wadda ya kafa ta tare da wasu fitattun ’yan jarida da nufin yaki da zalunci irin na siyasa da na zamantakewa.
A ranar 19 ga watan Oktoban 1986 ne wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kashe shi ta hanyar bam din da suka sa a cikin wasika.
- Dalilin da ba zan tsoma baki kan rikicin Masarautar Kano ba — Shekarau
- Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 12 a Borno
Shekara 38 bayan nan babu amo babu labari game da wadanda suka aikata kisan.
A ranar 16 ga Fabrairun 2024, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Gwamnatin Tarayya ta sake bude bincike a kan kisan Dele Giwa da sauran ’yan jaridar da aka kashe a yanayi na ban-mamaki da ke cike da sarkakiya.
James Bagauda Kaltho
Mista Kaltho, dan jarida kuma tsohon marubuci a mujallun Tell da Tempo, ya rasu a fashewar bam a otal din Durbar da ke Kaduna a ranar 12 ga watan Nuwamban 1995, shi ma a yanayi na ban-mamaki da sarkakiya.
Akwai bayanai masu karo da juna kan mutuwarsa. A watan Satumban 2022 ne matarsa ta roki Gwamnatin Tarayya ta sake bude bincike a kan mutuwarsa.
Aminoasari Dikibo
Aminosoari Dikibo fitaccen dan siyasa ne daga Jihar Ribas.
An bindige shi ne a shekarar 2007, yayin da yake tafiya daga Fatakwal zuwa Asaba don taron siyasa lokacin yana neman kujerar Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa, majiya daga iyalansa sun dora alhakin kisan a kan wasu manyan ’yan siyasa.
Binciken ’yan sanda kan lamarin ya haifar da kama wasu da ake zargi, amma har yanzu ba a samu cikakken sakamako ko kaiwa ga karshen lamarin ba.
Olaitan Oyerinde
Olaitan Oyerinde shi ne Babban Sakataren Ma’aikatan tsohon Gwamnan Jihar Edo, Adams Oshiomhole, har zuwa ranar 4 ga Mayu, 2012, lokacin da wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka bindige shi a gidansa da ke Birnin Benin na Jihar Edo.
’Yan sanda sun fara zargin abokin aikinsa kuma abokinsa, Rabaran David Ugolor, wanda ya raka matarsa zuwa asibiti don kula da lafiyarta.
Amma ya kalubalanci zargin da gwamnati ta yi masa na daukar nauyin kisan.
Bayan tsare shi, kotu ta wanke shi tare da sa ’yan sanda su biya shi diyyar Naira miliyan biyar.
Har yanzu ba a gano wadanda suka aikata kisan ba.
Bola Ige
Tsohon mai son tsayawa takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar AD A 1998, amma ba samu tikitin ba.
Daga baya Shugaban Kasa na lokacin Cif Olusegun Obasanjo ya nada shi Ministan Makamashi da Lantarki a 1999.
A ranar 23 ga Disamban, 2001 an bindige Bola Ige a gidansa a Ibadan, Jihar Oyo.
Bayanai sun ce a lokacin yana fama da takaddamar siyasa da jam’iyyarsa ta AD a Jihar Osun inda Gwamna Bisi Akande ke da matsala da Mataimakinsa Iyiola Omisore.
Bayan kisansa, ’yan sanda sun yi zargin kisan na da alaka da siyasa kuma sun kama mutane da yawa ciki har da Omisore bayan Shugaba Obasanjo ya tura sojoji don hana barkewar rikici sakamakon mutuwarsa.
Dukkan wadanda aka kama aka yanke musu hukunci kan kisan, ciki har da Omisore da Baba Fryo, an sallame su.
Har yanzu ba a gano ainihin wadanda suka aikata kisan ba.
An binne Ige a garinsu da ke Esa-Oke, Jihar Osun.
A wani jawabi lokacin binne shi, an ruwaito kalamansa cewa yana da yakinin cewa rayuwa a Najeriya tana da kima, amma ba ya da yakinin cewa tana da kimar da za a iya sadaukar da rai dominta.
Kudirat Abiola
Kudirat Abiola matar Cif Moshood Abiola ce da ake ganin ya lashe zaben Shugaban Kasa na 12 ga Yunin 1993 da gwamnatin Ibrahim Badamasi Babangida ta soke.
An kashe Kudirat yayin da mijinta ke tsare a hannun gwamnati a ranar 4 ga Yunin 1996.
An bindige ta ce yayin da take tafiya tare da mai taimaka mata da direbanta a cikin mota.
Direban ya rasu daga baya yayin da mai taimaka mata bai ji raunin komai ba wanda hakan ya haifar da zargin da ya kai ga kama shi da wasu mutane.
Ba a samu kaiwa ga karshen shari’ar ba bayan shekaru da dama na bincike da wadanda ake zargi a kai, ciki har da Manjo Hamza Al-Mustapha da Alhaji Lateef Shofolahan, wadanda aka wanke su daga zargin kisan da Kotun Daukaka Kara ta yi a Legas a watan Janairun 2012.
Funsho Williams
Funsho Williams fitaccen dan siyasa ne daga Jihar Legas kuma tsohon Kwamishina a lokacin tsohon Gwamnan Soja na Jihar, Kanar Olagunsoye Oyinlola.
A tsakiyar shekarun 1990 ya fara shiga jam’iyyar siyasa ta UNCP, amma daga baya ya koma Jam’iyyar AD bayan rasuwar Janar Sani Abacha.
Bayan wani dan lokaci Williams ya sake sauya sheka zuwa Jam’iyyar PDP, inda ya nemi tikitin takarar Gwamnan Jihar Legas a karkashin jam’iyyar.
A ranar 27 ga Yulin 2006 an samu Funsho Williams a gidansa da ke Dolphin Estate a Ikoyi, yankin masu kudi da ke Legas, an soka masa wuka.
An kama mutum biyu da suka hada da kodinetan yakin neman zabensa da abokin hamayyarsa a neman takarar Gwamna a PDP mai suna Adeseye Ogunseye a ranar 28 ga Yulin 2006, kan zargin kisansa.
Shi ma dai har yanzu ba a gano wadanda suka yi kisan ba.
Alfred Rewane
Alfred Rewane dan kasuwa ne kuma dan siyasa da aka sani da bayar da gudunmawa ga Kungiyar NADECO kuma aboki na kusa ga Cif Obafemi Awolowo.
A ranar 6 ga Oktoban 1995, an kashe shi a gidansa da ke Ikeja, Legas.
Yana tsakiyar ayyukan NADECO, inda gidansa ya zama wurin taron siyasa.
’Yan sanda sun kama mutum bakwai da ake zargi da kisan, amma mutum biyar sun mutu a tsare yayin da sauran biyu aka sake su bisa hujjoji masu rauni.
Marshal Harry
Harry Sokari Harry dan siyasa ne kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar All ANPP a Kudu maso Kudu.
A ranar 5 ga Maris, 2003, aka kashe shi a Abuja.
Kafin kisan, Harry shi ne Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Ribas, inda daga nan ya koma ANPP saboda kukan ba a gudanar da taron jam’iyyar.
Dansa mai suna Inye ya zargi tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo da tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Peter Odili, BABBAN LABARI Juma’a, 9 ga Agusta, 2024 kan kisan.
Duk da haka, ba a samu wanda ya aikata laifin ba.
Dipo Dina
Dipo Dina dan kasuwa ne, dan siyasa, mai taimakon jama’a wanda ya fito daga Jihar Ogun.
Shi masanin mulki ne, shugaban al’umma, kuma kwararren akanta.
A shekarar 2003 ya shiga siyasa inda ya shiga Jam’iyyar AC kuma ya samu tikitin takarar Gwamna a shekarar 2007.
A ranar 25 ga Janairun 2010 a hanyarsa ta zuwa gidansa da ke Dolphin Estate a Ikoyi Jihar Legas, aka sace shi sannan aka kai shi wani wuri da ba a san ina ne ba aka kashe shi.
An ce wadanda suka kai harin sun bar sauran fasinjoji biyu, ciki har da direbansa a raye.
Ba a samu wadanda suka aikata kisan ba kuma daga karshe babu wani bayani da ya fito.
Sunday Ugwu
Sunday Ugwu dan uwan tsohon dan Majalisar Dokokin Jihar Enugu, Barista Nwabueze Ugwu.
Dan majalisar na fama da rikici da Gwamnan Jihar, Chimaraoke Nnamani da wani bangare na majalisar.
A ranar 9 ga Satumban, 1999 aka kashe kaninsa Sunday Ugwu, mai shekara 38 inda ake zaton an yi hayar makasansa ne suka dauke shi bisa kuskure.
Mutuwar ta haifar da rikici a majalisar, kuma har yanzu ba a samu wadanda suka yi kisan ba.
Tordue Salem
Dan jaridar da ke aiki a Jaridar Vanguard, Tordue Salem ya bata bat na fiye da tsawon wata guda a Abuja, bayan ya fita a ranar 13 ga Oktoban 2021, kuma daga baya aka same shi a mace a ranar 10 ga Nuwamba, 2021.
’Yan sanda sun kama kuma suka nuna wani direban tasi a gaban jama’a, wanda ya ce a taron manema labarai cewa shi ya kashe Salem a wani hadarin mota.
Amma ba a ji komai game da lamarin ba tun bayan nan.
Nasir Rabe
Nasir Rabe tsohon Kwamishinan Kimiyya, Fasaha da Kere-Kere na Jihar Katsina, kafin wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba su ka kashe shi a gidansa a watan Disamban 2021.
Rabe ya taba zama jami’i a Hukumar Tsaron Kasa (SSS) da Hukumar EFCC a Abuja.
Ya kuma wakilci Mazabar Mani/ Bindawa a Majalisar Wakilai daga 2007 zuwa 2011.
Gwamnatin Jihar a karkashin Gwamna Aminu Bello Masari da hukumomin tsaro sun yi kokari sosai don gano wadanda suka yi kisan ba tare da cimma nasara ba.