✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada ‘yogurt’ na gida (Home made Yogurt)

Madarar yogurt na daga cikin kayan sha masu lafiya da amfani a jikin dan Adam. Ana yin yogurt ne daga madara da sauran kayan hadi.…

Madarar yogurt na daga cikin kayan sha masu lafiya da amfani a jikin dan Adam. Ana yin yogurt ne daga madara da sauran kayan hadi.

Ana shan sa haka ba tare da an sa wani abu a ciki ba; za kuma iya shan sa da sukari ko ’ya’yan itatuwa da dai sauransu.

Kayan hadi:

  1. Madara kofi hudu
  2. Ruwa kofi hudu
  3. Sukari kofi
  4. Flavor mai kamshin madara cikin cokali.
  5. Corn starch kofi daya
  6. Culture rabin cokali

Yadda ake hadin:

Da farko za a kwaba madarar (ta gari) da sukari da corn starch sai a zuba ruwan sanyi a kai.

Daga nan sai a tafasa ruwan zafi a zuba a kai, idan an dan dade sai a juya shi har sai an tabbatar babu kulalai ko kadan a ciki.

A murje hadin ya zama ruwa sannan a bar shi ya huce ya zama da dumi.

Kafin ya yi sanyi sosai sai a zuba culture a ciki.

Bayan an sa culture sai a rufe a bari ya yi awa takwas zuwa 12, ko ma ya kwana.

Idan aka bude shi sai a zuba sukari da flavor sai a motsa.

Idan yogurt din ya hadu sai a sa a fridge a bar shi ya yi sanyi.

Daga nan sai a sha shi yadda ake so.


Karin haske:

Za a iya amfanin da madarar gari ko ta ruwa wajen hada yogurt na gida.

Idan da madarar gari za a yi amfani, to yadda na yi bayani haka za a yi.

Idan kuma da madarar ruwa ce, to a dafa madarar sa’annan a diga mata culture, a rufe na tsawon awa takwas koh sha biyu.

Wannan shi ne yadda ake yin yogurt a gida daki-daki.

Za ku kuma iya sha da fura ko a kankare kwakwa a ciki yogurt din a sha da shi.