✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka miyar wake

A yayin da azumin watan Ramadana ya kan-kama, Aminiya za ta ci gaba kawo yadda ake yin wasu girke-girke domin magidanta su amfana. A yau…

A yayin da azumin watan Ramadana ya kan-kama, Aminiya za ta ci gaba kawo yadda ake yin wasu girke-girke domin magidanta su amfana.

A yau mun kawo muku yadda ake yin miyar wake, wadda ana iya hada ta da abinci iri-iri musamman turo, sakwara, teba da sauransu.

Ga abubuwan da ake bukata wajen girka miyar wake:

Wake

Manja

Tumatir

Attaruhu

Tattasai

Bushenshen kifi

Albasa

Dunkulen sunadarin dandano

Kori

Gishiri

Yadda ake hadawa

Da farko za ki surfe wake ki wanke ya fita sosai, sai ki dora ruwa a wuta ya tafasa sai a zuba waken ya yi ta dahuwa har sai ya nuna ya yi taushi sosai

Sai a soya manja a wuta ya yi zafi sannan a zuba jajjagaggen kayan miya da albasa da manja da kifi.

Sai a sa maggi da kayan kamshi (kori da tyme) da gishiri, sai ki barshi yana turara har zuwa tsawon minti sha biyar.

Da zarar a duba miyar ta yi gwargwadon bukatar soyuwa sai a sauke

Za iya ci da tuwon shinkafa ko masara ko semobita ko waina.