A yayin da azumin watan Ramadana ya kan-kama, Aminiya za ta ci gaba kawo yadda ake yin wasu girke-girke domin magidanta su amfana.
A yau mun kawo muku yadda ake yin miyar wake, wadda ana iya hada ta da abinci iri-iri musamman turo, sakwara, teba da sauransu.
Ga abubuwan da ake bukata wajen girka miyar wake:
Wake
Manja
Tumatir
Attaruhu
Tattasai
Bushenshen kifi
Albasa
Dunkulen sunadarin dandano
Kori
Gishiri
Yadda ake hadawa
Da farko za ki surfe wake ki wanke ya fita sosai, sai ki dora ruwa a wuta ya tafasa sai a zuba waken ya yi ta dahuwa har sai ya nuna ya yi taushi sosai
Sai a soya manja a wuta ya yi zafi sannan a zuba jajjagaggen kayan miya da albasa da manja da kifi.
Sai a sa maggi da kayan kamshi (kori da tyme) da gishiri, sai ki barshi yana turara har zuwa tsawon minti sha biyar.
Da zarar a duba miyar ta yi gwargwadon bukatar soyuwa sai a sauke
Za iya ci da tuwon shinkafa ko masara ko semobita ko waina.