Assalamu Alaikum Uwargida. Yau a filinmu na Girke-girken Azumi, za mu kawo miki yadda ake girka Miyar Oha.
Ga wasu daga cikin kayan hadin da ake bukata don yin miyar:
- Malamin da ake zargi da azabtar da almajirinsa a Kano ya shiga hannu
- Ahmed Lawan ya roki ’yan Najeriya su sake ba APC dama a 2023
Ganyen Oha
Gwaza kanana kamar guda takwas
Manja kamar cokali uku
Naman shanu
Kayan ciki
Ganda
Busasshen kifi
Barkono
Sinadarin dandano
Kifin ‘crayfish’
Yadda za a hada kayayyakin
A dafa kayan ciki da busasshen kifi da ganda ta yadda za su yi laushi.
Sannan a wanke naman shanu a zuba a tukunyar da kayan cikin ke ciki da sauran kifin.
A ci gaba da dafa su har sai naman ya nuna.
Sai a zuba sinadarin dandano kamar guda biyu sannan a ci gaba da dafawa na tsawon minti biyar.
Sannan a zuba dakakken barkono da dakakken crayfish.
A ci gaba da dafa su na kamar tsawon minti 10.
Sai a tafasa gwaza a kwaba ta a ruwa kadan a zuba.
A ci gaba da dahuwar sannan a zuba manja a rufe tukunyar har sai miyar ta dan yi kauri.
Za a iya kara ruwan zafi idan miyar ta cika kauri sannan a gauraya.
Sai a tsinka ganyen na Oha da hannu kuma a yanka shi da hannu, ba da wuka ba domin kada ganyen ya yi baki sannan sai a gauraya.
Za a iya cin wannan miyar da sakwara ko tuwon semovita.