✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake amfani da sabulun salo don gyaran fata

Yana da kyau mata su san yadda ake hada irin wannan sabulun domin gyaran jiki ko kuma don sana’a. Yawan shafe –shafe yana bata fatar…

Yana da kyau mata su san yadda ake hada irin wannan sabulun domin gyaran jiki ko kuma don sana’a. Yawan shafe –shafe yana bata fatar jiki don haka idan ana shafa abu kadan a fatar jiki, ya fi amfani da kuma gyaran fata. A yau mun kawo muku hanyoyi daban-daban wadanda za a yi amfani da sabulun salo don gyaran fata .

Abubuwan da za a bukata
•Sabulun salo
•Zuma
•Bitamin E
•Man almond (za a iya samun sa a shagunan kayan kwalliya)

Hadi
A daka sabulun salon ko kuma a saka abin kankare kubewa a kankare. Sannan a zuba ruwa domin ya narkar da sabulun. Sannan a zuba ‘bitamin E’ da man ‘almond’sai a kwab su sosai. Irin wannan hadin na gyara fatar jiki da kuma sanya ta subul da laushi.

Hadi na 2
•Sabulun salo
•Man kadanya
•Ruwan ganyen ‘aloe bera’
A narka man kadanya a ruwan zafi sannan a narkar da sabulun salon shi ma. A samu gora a zuba hadin man kadanyar tare da na man kadanya da ruwan ganyen ‘aloe bera’ sannan a girgiza su domin su hadu sosai.
Za a iya amfani da shi nan take daga gama hadi ko kuma a zuba a bar shi tsawon sati biyu sannan a fara amfani da shi.

Hadi na 3
•Sabulun salo
•Zuma
•Kurkum
•Man kwakwa
•Man Zaitun
Bayan an narkar da sabulun salo a ruwan zafi, sai a zuba zuma da kurkum da man kwakwa da kuma man zaitun. A zuba su a cikin gora sannan a girgiza sosai domin su hadu sosai,sannan sai a zuba a murta.
Za a iya amfani da wannan hadin nan take ko kuma a jira ya yi tauri bayan sati biyu sannan a fara amfani da shi.
Wannan hadin yana magance kurajen gumi ko na fuska da wasu cututtukan fata.