✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake alalar shinkafa

Bayani dalla-dalla kan yadda ake dafa alalar shinkafa, dafa farko har zuwa karshe

Ga bayani dalla-dalla, daga farko har karshe, kan yadda ake dafa alalar shinkafa.

Kayan hadi

  • Shinkafar tuwo
  • Nama ko kifi
  • Man gyadda
  • Manja
  • Tattasai
  • Attarugu
  • Albasa mai lawashi
  • Kori
  • Thyme
  • Kwai
  • Magi
  • Gishiri

Yadda ake hadin

– A wanke shinkafa a shanya ta bushe, sai a nika ta a a tankade.

– A samo roba mai zurfi a zuba garin shinkafar a cikin sai a zuba ruwa a kwaba kamar kwabin kullun kosai.

– A yayyanka dafaffen kwai a zuba a ciki.

– Zuba dakankken kayan miya, sai a yayyanka albasa da lawashi kanana a ciki.

– A zuba kayan dandano da man gyadda da man ja dadai yadda ake bukata.

– A marmasa nama ko kifi a zuba a ciki, sannan a zuba kori da thyme a juya soai kullun ya hadu sosai.

– Sai a samu gwangwani ko leda a zuba a cikin dai dai yadda ake so.

– Sanya tukunya a wuta sai a zuba ruwa a ciki.

– Idan ruwan ya tafasa sai a zuba kullin alalen a cikin, a rufe sosai da leda ko gyanyen ayaba.

– A bari a kan wuta har sai ya nuna sosai.

Shi ke nan sai a ci dadi lafiya.

Ku ma kuna iya jarawaba.