✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi wa Bakano ruwan N250m saboda mayar da kuɗin tsintuwa

Na yi matukar murna saboda ban tsammaci mayar da kudin zai jawo min irin wannan daukaka ba.

Bakanon nan mai tuka Keke NAPEP ko A Daidaita Sahu mai suna Auwalu Salisu, wanda ya mayar da kudin tsintuwa har Naira miliyan 15 ga mai shi, kakarsa ta yanke saka, inda aka yi masa ruwan Naira miliyan 250 tare da daukar nauyin karatunsa har zuwa matakin digirin digirgir.

Kamfanin Jaridun LEADERSHIP Media Group ne ya karrama Auwalu da lambar yabo a matsayin “Fitaccen Matashin Shekarar 2023” a ranar Talatar makon jiya a Abuja, sakamakon nuna gaskiya da rikon amana wajen mayar da Naira miliyan 15 ga wanda ya hau A Daidaita Sahunsa kuma ya mance da su.

Daga farko dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi da Mataimakinsa, Datti Baba Ahmed ne suka bayyana daukar nauyin karatun Auwal Salisu.

Peter Obi da Datti sun dauki nauyin Auwalu mai shekara 22 har sai ya kammala karatu a Jami’ar Baze mai zaman kanta da ke Abuja, inda za su rika biya masa kudin makaranta da na abinci da na dakin kwana da masa sauran bukatu.

Sai Gwamnan Jihar Neja Mohamammed Umar Bago, wanda aka karrama a matsayin “FItaccen Gwamnan Shekara ta 2023” ya bayyana bayar da tallafin karatu na Naira miliyan 250 ga Auwalu saboda nuna halin gaskiya, inda ya bukaci matasan Nijeriya su yi koyi da shi.

Gwamna Bago ya ce, Auwalu zai samu tallafin karatu na Naira miliyan 50 daga gare shi, sai wata miliyan 50 daga Shugaba Bola Tinubu, sai ministocinsa Naira miliyan 50 sai gwamnonin APC Naira miliyan 50, sai kuma gwamnatin Jihat Neja Naira miliyan 50.

Gwamna Umar Bago ya ce zai kuma sanya wa daya daga cikin titunan da yake ginawa a Neja sunan Bakanon mai tuka A Daidaita Sahu kuma dan wani mahauci.

Da yake nuna jin dadi da godiyarsa kan lambar girmamawar, Auwalu ya ce lambar fitaccen matashi ta LEADERSHIP daya ce daga cikin karramawa da dama da ya samu tun lokacin da ya mayar da Naira miliyan 15 da ya tsinta a A Daidaita Sahunsa ga mai su dan kasar Chadi.

“Ina yabo da godiya ga Jaridar LEADERSHIP kan wannan karramawa. Na yi matukar murna saboda ban tsammaci mayar da kudin ga mai su zai jawo min irin wannan daukaka ba.

“Duk da cewa yunwa ba za ta bar wasu mutane su mayar da kudin ba, amma akwai bukatar ka fi karfin zuciyarka, saboda ta fi komai.

“Na samu kyaututtuka da lambobin yabo da daga mutane dama ciki har da ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano da Mai martaba Sarkin Kano, bayan na mayar da kudin ga mai su.

“Kuma wannan karramawa ta LEADERSHIP shaida cewa yana da kyau mutum ya ksance mai gaskiya,” in ji Auwalu.

Masu shirya taron bayar da lambobin yabo a taron Shekara-Shekara na LEADERSHIP, sun ce a kasar da matasan yanzu da dama ba su dauki gaskiya da muhimmanci ba, Auwalu ya sake farfado da kyakkyawar fata ga manyan gobe ta wajen nuna gaskiya da rikon amana.

Auwalu ya mayar da kudin da fasinjan ya bari a cikin babur dinsa ne bayan ya ji cigiyar kudin a gidan rediyo.

Wani dan kasuwa dan kasar Chadi da ya je Kano yin sayayya ne ya manta kudin a cikin babur din.