Wata mata mai suna Toyin Oseyemi, wadda mijinta Mista Oseyemi Sunday Olanrewaju ya rasu a ranar 10 ga Afrilun, 2021 a asibitin Bicar Clinic da ke Abuja, ta tsinci kanta cikin ukubar al’adun takaba na dangin mijinta bayan rasuwarsa.
Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa, bayan Toyin ta lura mijinta na numfashi sama-sama kuma yana tari mai jini, ta garzaya da shi asibitin kuma nan take likitoci suka daura masa ledar ruwa da ta jini, amma bayan minti 45 ya ce ga garinku nan.
Yayin da hakan ya jefa Toyin cikin alhinin rasa mijinta kuma uban ’ya’yanta, sai kuma ta ci karo da wani kalubale na daban lokacin da suka je bikin binne marigayin a kauyensa da ke Jihar Ondo.
Majiyar ta ce Toyin da sauran wadanda suka raka gawar marigayin suna isa garin aka binne shi a ranar 17 ga Afrilu, 2021.
Kuma bayan binne shi ne aka fara wasu al’adu na mutanen garin Ondo, inda da farko aka tilasta wa Toyin kaurace wa amfani da ruwa na tsawon kwana tara.
Wato ba za ta yi wanka da ruwa ba kuma ba za ta wanke baki ba, ko duk yin wani abu da zai sa ta taba ruwa.
Bayan wannan an kuma tilasta mata zama a dandamalin kasa na kwana tara.
Kuma wani babban abin bakin ciki shi ne an tilasta wa Toyin kwana-zaune na tsawon kwana tara, saboda mutanen Ondo sun camfa cewa ko gyangyadi ta yi marigayi mijinta zai bayyana gare ta.
Kuma a lokacin da take shirin dawowa Abuja tare da ’ya’yanta mata uku ne sai aka shaida mata cewa da sauran rina a kaba, yanzu ta ci nasarar kammala kashi na farko ne na jana’izar marigayin, kashi na biyu zai gudana ne na tsawon wata uku.
Toyin da ’ya’yanta sun shiga tasku ba wai kawai kan rasa miji kuma uba ba, a’a sai dai kari a kan haka na haduwa da wata tsohuwar bakar al’ada.
Domin a lokacin an shawarci Toyin cewa kada ta kuskura ta je kowace kasuwa har tsawon kwana 90, in ba haka ba kurwar mijin za ta rika bayyana tana gallaza mata.
Hakika abin al’ajabi ne a ce har yanzu ana aiki da irin wannan al’ada, kuma a tilasta ma’aikaciya ta yi aiki da ita.
Yanzu haka dai Toyin tana ta jimamin abin da dangin mijinta za su kakaba mata a yayin da take cikin zango na biyu na gudanar da al’ada.