✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka gudanar da wasan dambe lokacin bikin Sallar Layya a Zariya

Aminiya ta ziyarci gidan wasan damben gargajiya wanda ake yi a kowace yammaci a gidan wasan kwallon kafa da ke layin (Club Street) a karamar…

Aminiya ta ziyarci gidan wasan damben gargajiya wanda ake yi a kowace yammaci a gidan wasan kwallon kafa da ke layin (Club Street) a karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna, kuma wakilinnmu ya tarar da masu sha’awar kallon wasan sun yi layi suna karbar tikitin shiga filin wasa domin ganin wasan bikin sallah.   

Gidan dambe wanda ya cika makil da ’yan kallo, da kuma bakin shahararrun ‘yan wasan damben gargajiya daga sassan kasar nan, wanda suka hada ‘yan wasa daga bangaren Arewa da kuma yankin Kudu, kuma manyan ‘yan wasa ne daga sassan biyu suka halarci bukin wasan sallah a garin na Zariya.

’Yan wasan sun kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dokta Shehu Idris ziyarar gaisuwar barka da sallah a fadar sa kafin su fara gudanar da gasar su.

Aminiya ta tattauna da wasu daga cikin manyan ’yan wasan daga bangaren Arewa da Kudu.   Na farko shi ne shahararan dan wasan dambe daga Kudu kuma wanda yake cin zamaninsa domin yanzu ba kamarsa a harkar damben gargajiya,  wanda ya lashe kyaututtuka da dama ga kuma bayani daga bakinsa. “ Sunana Muhammadu Abdurrazak  amma a harkar dambe  ana kirana da Ebola, kuma ni dan asalin Jihar Kaduna ne.   Nagode Allah domin da ina zuwa kallon wasan dambe ne sai ga shi cikin ikon Allah Ya sa na shahara a harkar dambe domin duk inda ake wasan dambe a kasar nan babu inda ban je ba kuma duk inda Allah Ya kai ni sai na zama zakara, domin na ci gasar dambe da dama.   Na farko shi ne wasan  dambe na Unguwar Dei-dei da ke Abuja wanda na kashe Jirgin Bahago aka ba ni kyautar rago, sai wasan Fashon a garin Suleja wanda na kashe Shamsu kanin Eabi na samu kofi da kudi Naira dubu dari, sai wasan garin Mina inda na kashe Soja Dogo Jambo aka ba ni kyautar Naira dubu dari da hamsin.  Sannan a garin Maraban Nyanya na kashe Dogon Kelle aka ba ni kyautar bijimin Sa, sai damben garin Kano wanda muka yi a karamar sallah bara muka buga da Bahagon Sani Kurna na kashe shi na samu kyautar mota da kujerar Hajji, kuma mai girma Gwamna Kano Abdullahi Ganduje ya sa kyautar mota ita ma na lashe.   Wasan da na ci na karshe shi ne wasan damben karamar Sallah na  garin Kano an sa kyautar mota CRb na lashe, kuma yau kimanin kwanana goma kenan a garin Zariya na yi dambe tara na lashe takwas duk da damben da na yi a gabanka wanda na kashe Zakari Isa Abba Shagon Shamsi.

Wakilin Aminiya ya ga yadda aka goge raini a tsakanin gogagun ’yan wasa wadanda suka yi fice a damben gargajiya kamar na  Zakari Isa Shagon Shamsi daga Arewa, da kuma Muhammadu Abdurrazak Ebola daga Kudu, wanda a zagaye na biyu Abdurrazak Ebola ya kashe Isa Aba Shagon Shamsi.

Bayan kammala wasan tsakanin gogagun ‘yan wasna Aminiya ta ji ta bakin mai masaukin bakin, kuma maigidan dambe mai suna Anas Sadauki dan Sarkin Fawa inda ya ce,”To kamar yadda kake gani mun gayyaci manyan bakin ’yan dambe daga kowace kusurwa ta kasar nan domin mu kai wa Mai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris gaisuwar sallah, sannan don mu kawata bikin sallah a garin Zariya. To Alhamdulillahi domin bukatar mu ta biya manyan ‘yan wasan mu sun yi dambe a gaban Mai Martaba Sarki, kuma Sarki ya ji dadi, kuma jama’a da dama sun amfana musamman ’yan kasa, kuma idan ‘yan wasamu suka gama isowa za mu sa gasar cin mota in Allah Ya so.   Mu dai fatarmu a koyaushe shi ne masu sha’awar wasan damben gargajiya su ci gaba da ba mu hadin kai, kuma muna fata a tashi lafiya.

Wasu da suka kalli yadda wasannin damben suka gudana sun yaba da yadda aka shirya damben, kuma sun nuna abin ya kayatar musamman an yi wasannin ne a lokacin da aka yi shagulgulan sallar layya.