Wani manazarci a kan lafiyar kwakwalwa, Dokta Willie Stewart, ya yi gargadi kan yadda ’yan kwallon kafa suke dukan kwallo da ka, yana mai nuni da hatsarin yin hakan.
Dokta Stewart wanda shahararren mai bincike a game da alakar cutar mantuwa da wasannin motsa jiki, ya yi kira ga mahukuntan wasan kwallon kafa da su yi nazari a kan haramta dukan kwallo da ka saboda hatsarin da hakan ya kunsa.
Goal.com ta ruwaito jami’in na Jami’ar Glasgow da ke Birtaniya yana cewa, kamata ya yi yanzu a rika fitar da sakonni na kashedi a kan hadarin dukan kwallo da kai ga ’yan wasa.
Binciken da aka gudanar a baya ya nuna cewa, karin ’yan wasa na cikin hadarin mutuwa saboda cutar mantuwa ta dementia ko kuma saura cututtuka da suka shafi kwakwalwa fiye da sauran al’umma.
Stewart ya ce a kan haka ne wani sabon bincike da aka wallafa a Mujallar JAMA Neurology ya bayyana matakan da ya kamata a dauka dangane da lamarin.
Cikin tsaffin ’yan wasa 7676 da aka gudanar da bincike a kansu, kasha hudu cikin 100, wato 386 sun kamu da cutar da ta shafi kwakwalwa da mantuwa.
Kazalika, binciken wanda aka fitar a makon nan ya nuna cewa hadarin ya danganta da inda dan wasa ke bugawa a filin wasa da tsawon lokacin da suka shafi suna murza tamaula, inda galibi ’yan wasan baya sun fi kamuwa da cutar.
A kwanan nan ne Hukumar Kwallon Kafa ta FA da ta Firimiyar Ingila, suka fidda sabuwar doka kan wannan lamari game da ’yan wasan kwallon kafa yayin basu horo da motsa jiki.
Sabuwar dokar ta shawarci kungiyoyin kwallon kafa da suka iyakance yawan dukan kwallon da ka da kowane dan wasa zai yi yayin karbar horo zuwa 10 a duk mako.
Wannan sabuwar doka ta shafi dukkan kungiyoyin kwallon kafa a kowane mataki.
A makon nan ne Manajan Kungiyar Accrington, John Coleman ya ce za a iya haramta wa ’yan wasa dukan kwallo da ka nan da shekaru goma masu zuwa.
Coleman mai shekaru 58 ya ce haramta wa yan wasa dukan kwallon da ka zai taimaka matuka wajen rage yawan kamuwa da cututtukan da suka shafi kwakwalwa.