✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya tsiyaye wa matashi ido

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Sabon gari a Jihar Kano ta tura wani matashi mai suna Nura Lawan Makafin Dala ajiya a gidan kaso…

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Sabon gari a Jihar Kano ta tura wani matashi mai suna Nura Lawan Makafin Dala ajiya a gidan kaso bisa zarginsa da fasa idon wani matashi mai suna Mustapha Abubakar Kura lamarin da ya yi sanadiyyar tsiyayewar idon gaba daya.

A kwanakin baya ne wanda ake zargin ya kama Mustapha inda ya yi amfani da karfi ya fasa masa idanu a daidai lokacin da wata hatsaniya ta faru a tsakaninsu.

Sai dai wanda ake zargi ya musanta aikata laifin da ake zaginsa wanda ya saba wa sashe na 167 na Final Kod.

Alkalin Kotun Mai shari’a Muhammad Hussaini Kurawa ya dage shari’ar zuwa yau Juma’a.