✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya saki matarsa saboda ta fiye zafin rai

Ta fiye matsala kuma kullum sai ta yi fada da ni, inji mijin.

Wata Kotun yanki mai daraja ta daya da ke Kubwa, Abuja, ta raba auren shekara takwas tsakanin wasu ma’aurata, saboda matar na da zafin rai.

A karar da ya shigar, mijin matar wanda suke da da, ya roki kotun da ta raba auren saboda matar tasa ta addabe shi da yin fada kullum.

“Matata mace ce mai matsala, ba ta bari na in huta ba kuma kullum sai ta yi fada da ni, saboda haka na sake ta saki uku,” inji shi.

Matar ta amince da saki, wanda alkalin kotun, Muhammad Adamu ya tabbatar.

Da yake zartar da hukunci, Adamu ya umarci matar da ta yi zaman “Iddah” na tsawon watanni uku kafin ta sake aure.