✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya saci zakara saboda bai ci nama ba tun farkon Azumi

Tunda watan azumi ya kama ban ci nama ba.

Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Unguwar Dambare a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi hukuncin bulala ashirin sakamakon samunsa da laifin satar Zakara.

Bayan gurfanar da matashin, an karanto masa kunshin tuhumar da ake yi masa inda nan ta ke ya amsa laifin.

Ya kara da cewa kwadayinsa ne ya tashi domin tunda aka fara Azumin bana bai ci nama ba.

Jami’an ’yan sanda ne suka gurfanar da matashin mai suna Nazifi Hassan a gaban kotun karkashin jagorancin mai shari’a Mallam Munzali Idris Gwadabe.

An kama matashin ne a Unguwar Gwazaye da ke Karamar Hukumar Kumbotso ta Kano, yayin da ya saci Zakaran a kofar wani gida kuma tuni kotun ta bayar da umarnin a ba wa mai Zakaran kayansa.