Shugaban Kungiyar Tsaro da Yaki da ’Yan fashi da Sauran Masu Aikata Miyagun Ayyuka ta Danga da ke Karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi, Malam Yusuf Abdullahi Magama ya yi kira ga sabon Gwamnan Jihar Sanata Bala Mohammed cewa da zarar an rantsar da shi, ya tallafa wa kungiyoyin tsaro na sa-kai da ke jihar don a magance matsalar tsaro da ake fama da shi.
Malam Yusuf Abdullahi Magama ya yi wannan kira ne lokacin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce, akwai barazanar tsaro a jihar, musamman a yankin Toro domin a kowanne lokaci ana fashi da makami da garkuwa da mutane da sace-sace.
A cewarsa shi kansa al’amarin ya shafe shi a bara, inda wadansu barayi suka kawo masa hari suka kashe yaransa uku tare da kona gidansa.
Malam Yusuf, ya ce a wannan hari da aka kawo masa ya yi asara ta kusan Naira miliyan 23, amma Naira dubu 500 kawai gwamnati ta tallafa masa, aka ce ya saurara amma har zuwa wannan lokaci, babu wani tallafi da aka kara yi masa.
“Gaskiya harkokin tsaro a wannan yanki babu kyau, domin yau za ka ji an ce masu garkuwa da mutane sun zo sun tafi da mutane ko ka ji ’yan fashi da makami sun zo sun yi fashi musamman a garin Magama Gumau. Da gwamnati tana ba mu tallafi, tana kula da mu da an samu saukin wannan matsala. Domin daga lokacin da wannan kungiya ta zo zuwa yanzu, mun samu nasarar rage yawan fashi da makami da sace sace a wannan yanki,” inji shi.
Yusuf Danga ya ce, akwai alamun sabuwar gwamnatin da Kauran Bauchi zai kafa za ta tallafa wa kungiyoyin tsaro a jihar. Domin sabon Gwamnan yana tallafa wa irin wadannan kungiyoyi, tun kafin Allah Ya ba shi nasara.
Ya kara da cewa, idan sabuwar gwamnatin ta tallafa wa wadannan kungiyoyi, za a samu nasarar magance matsalolin fashi da makami da garkuwa da mutane da sace sace a jihar.