Labarin almajiri Nuhu Sale (ba sunan shi na asali ba) da ya rasa idonsa na hagu a Kano guda ne cikin labaran ban tausayi na rayuwar almajirci.
Watanni biyu da suka gabata idan ba a manta ba, wani malamin makarantar allo ya zane dalibinsa (almajiri) har sai da yai masa rauni.
- Tarayyar Afirka ta taya Macron murnar sake lashe zaben Faransa
- Kudin fansa: Masu garkuwa da ‘Uwar Marayu’ na neman N100m
A nasa bangaren Almajiri Nuhu na tafiya kan titi ne domin nemo abin sakawa a bakin salati inda ya gamu da wannan mummunan al’amarin.
Ya ce, “Ina cikin tafiyata sai yaron ya tunkaro ni ya ce zai saka ni aiki idan na gama ya ban abinci. Sai ya kai ni wani daji da ke kusa ya kwakule idona ta karfi da yaji.”
Wanda ake zargin mai suna Isah Hassan da Rundunar ’Yan Sandan Kano ta yi holensa ya ce ya daure hannun almajirin ne kafin ya sa wuka ya kwakule masa idon.
Ya kuma ce wata bokanya mai suna Furera ce ta ce ya kawo idon domin hada masa layar bata, da kuma kare shi daga hadurran daji kasancewarsa mai aikin gawayi a dajin.
Ya ci gaba da cewa, “Jikanta ne ya hada ni da ita, da na je na yi mata bayani ta ce idon mutum ne sinadarin layar. Bayan na cire idon sai ta ce sai na ba da N500, ni kuma ba ni da ita, don haka na koma da idon har sai da aka kwana biyu na samu.
“Matsalar da aka samu lokacin idon ya lalace, sai na fasa shi na saka a gorar da na cika da ruwa,” inji shi.
Sai dai mai ba da maganin gargajiyar, Hajiya Furera, mai shekara 100 ta musanta wannan ikirari, inda ta ce magani kawai ta ba shi na kurajen da suka fito masa.
Ta kara da cewa, “Da ina son aiki da idon wani, cikin jikokina 50 zan samu daya na cira.”
Abin lura: Mun sakaya suna yaron, ba mu yi amfani da sunan shi na ainihi ba.