✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ya kashe alkalin wasa saboda jan kati

Wani abu mai kama da almara ya faru a Ajantina a karshen makon jiya bayan wani dan kwallo ya bindige alkalin wasa jim kadan bayan…

Wani abu mai kama da almara ya faru a Ajantina a karshen makon jiya bayan wani dan kwallo ya bindige alkalin wasa jim kadan bayan ya ba shi katin kora (Red Card).
Al’amarin ya faru ne a wani yanki da ake kira Cordoba da ke Ajantina.  Rahoton ya nuna ana cikin wasa ne sai dan kwallon ya yi keta da hakan ta sa alkalin wasan ya ba shi jan kati kai tsaye.  Fitar dan kwallon daga fili ke da wuya sai ya nufi inda ya ajiye kayansa inda ya dauko bindiga kuma ya sake komawa cikin filin kuma kafin ka ce kwabo ya dirka wa alkalin wasan harsashi a kai da kirji da kuma a cinya inda nan take ya fadi matacce.
Nan take sauran ’yan wasa da ’yan kallo kowa ya yi ta kansa kuma wanda ya aikata laifin ya shiga cikin rububi ya sulale ya gudu ba tare da an kama shi ba.   Rahoton ya nuna harsashin da ya kashe alkalin wasan ya yi tsalle ya kuma shafi daya daga cikin ’yan kwallon mai suna Walter Zerate wanda shi ma aka garzaya da shi asibiti don yi masa magani.
Wani jami’in ’yan sanda da ke kula da yankin ya tabbatar da faruwar al’amarin inda ya ce: “Ba mu san abin da ya faru ba ana cikin yin kwallo sai muka ji tashin bindiga, kafin mu ankara sai muka hangi alkalin wasa a kasa magashiyyan yayin da wani daga cikin ’yan kwallon kuma ya zube a kasa yana ihun neman taimako”. Kafin mu ankara sai muka ga kowa ya ranta cikin na-kare ciki har da wanda ya yi harbin kuma ba mu samu nasarar kama shi ba”.
Sai dai jami’in ya ce yanzu haka rundunarsu ta baza komarta don ganin ta damko wanda ya yi kisan don ya fuskanci hukuncin da ya dace da shi.
Al’amarin yin kisa a lokacin kwallo a kasar Ajantina ba sabon abu ba ne, don irin hakan  ta sha faruwa a lokuta da dama.