Kungiyar nan mai rajin kare muradun ’yan kabilar Ibo, wato Ohanaeze Ndigbo, ta ce kamata ya yi a saka tsarin karba-karbar Shugabancin Najeriya tsakanin shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida a cikin Kundin Tsarin Mulki.
Kungiyar ta ce yin hakan shi ne zai tabbatar da adalci da da daidaito da kuma ganin ba a ci gaba da ware wani sashe na kasar ba.
- An shigo da madarar Naira biliyan 27 Najeriya cikin wata 3
- Wahalar fetur ta sa an mayar da hutun mako kwana 3 a Sri Lanka
Shugaban kungiyar, Cif Emmanuel Iwuanyanwu, ne ya bayyana hakan yayin wata zantawarsa da manema labarai a Abuja ranar Lahadi, bayan kammala taron kungiyar na musamman.
Ya ce batun yin karba-karba tsakanin Kudu da Arewa kawai tsarin danniya ne, kuma ya kamata a yi watsi da shi.
Iwuanyanwu ya ce idan za a yi adalci, da aka ce mulkin Najeriya a 2023 zai koma Kudancin Najeriya, kamata ya yi a bar wa yankin Kudu maso Gabas, kasancewar Kudu maso Yamma da Kudu maso Kudu sun taba danawa a baya.
Ya ce dattawan yankinsu sun yi iya bakin kokarinsu wajen neman ragowar yankunan biyu su hakura su ba su damar samar da Shugaban Kasa, amm suka ki.
A cewar Shugaban na Ohaneze, “Amma abin takaici, sai ’yan siyasa, ba dattawa ba, suka dauki wani matakin da ya ci mana dunduniya.
“Muna da tabbacin dukkan dattawan Kudancin Najeriya da na yankin Middle Belt sun goyi bayan a samar da Shugaban Kasa daga kabilar Ibo a 2023.
“Saboda haka, ra’ayina shi ne kamata ya yi a saka tsarin karba-karba a cikin Kundin Tsarin Mulki kuma ya rika zagayawa tsakanin shiyyoyin siyasar kasar nan guda shida.
“Abin tambayar a nan shi ne karba-karba tsakanin Kudu da Arewa na da tarnaki saboda ba ya tabbatar da tsarin raba daidai yadda ya kamata,” inji Iwuanyanwu said.
(NAN)