Sakataren kungiyar ’Yan kasuwar Arewa da suke zuwa Kudancin kasar nan don sayo ’yan kunne da sauran kayayyakin kwalliya, Alhaji Bashir Uba Hassan ya bayyana cewa sun kafa kungiyarsu ne don yin magana da murya daya.
Alhaji Bashir ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce domin a duk lokacin da ’yan uwanmu ’yan kasuwa na Kudancin kasar nan suka kira ’yan kasuwansu kan wani abu sakamakon yadda suke tafiya da murya daya nan take suke amsa kira.
“Amma mu a nan Arewa a baya abin ba haka yake ba, idan muka yi kokarin mu hada kan ’yan kasuwarmu sai ka ga wasu sun fandare. Amma yanzu sakamakon kafa wannan kungiya mun fara samun hadin kai, domin a lokacin da muka kira yajin aiki na kauracewa zuwa Kudancin kasar nan, kwanakin baya nan take ’yan kasuwarmu suka ba da hadin kai. Don haka mun fara samun narasa kan wannan kungiya da muka kafa,” inji shi.
A karshe sakataren ya yi bayanin cewa babban burin wannan kungiya shi ne ta tallafawa ’yan kasuwar Arewa ta kowace fanni.
‘Ya dace ’yan kasuwan Arewa su hada kansu’
Sakataren kungiyar ’Yan kasuwar Arewa da suke zuwa Kudancin kasar nan don sayo ’yan kunne da sauran kayayyakin kwalliya, Alhaji Bashir Uba Hassan ya bayyana…