✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya dace ’yan kasuwa su ji tsoron Allah’

An yi kira ga ‘Yan Kasuwa a Jihar Nasarawa da su ji tsoron Allah su daina fakewa da sadar Dalar Amurka suna kara farashin kayayyakinsu.Shugaban…

An yi kira ga ‘Yan Kasuwa a Jihar Nasarawa da su ji tsoron Allah su daina fakewa da sadar Dalar Amurka suna kara farashin kayayyakinsu.
Shugaban kungiyar ’yan kasuwan karamar Hukumar Akwanga da ke Jihar, Alhaji Sani Sunusi ne ya yi wannan kira a lokacin da yake tattauna da wakilinmu a garin Akwanga.
Ya ce: “addinin Musulunci da na Kirista sun hana karin farashin kayayyakin kasuwa fiye da kima.” Daga nan ya shawarce su da su daina yin haka don gujewa fushin Ubangiji. A cewarsa idan aka yi la’akari da yadda rashin kudi da al’ummar kasar nan ke fuskanta a halin yanzu sakamakon faduwar farashin man fetur, “bai kamata ana kara farashin kayayyakin ba gaira, ba dalili ba,” inji shi.
Kodayake, ya ce akwai abubuwa da dama da suka sa farashin kayayyaki suka tashi wadanda suka hada da faduwar farashin danyen man fetur da karin kudin kayayyaki da kamfononi da ke sarafa kayayyakin kasuwa suna karuwa akai-akai.
“A duk lokacin da aka fuskanci hakan wajibi ne ’yan kasuwa suma su kara farashin kayayyakinsu, amma a cewarsa bai kamata su rika yin haka fiye da kima ba,” inji shi.
Da yake bayyani game da matsaloli da ’yan kasuwar ke fuskanta a halin yanzu, Shugaban ya ce wadannan matsaloli sun hada da karancin shaguna a kasuwar don a cewarsa tun da gobara ta ci kasuwar kwanakin baya, inda ta cinye kimanin shaguna 480. Kodayake, ya ce a yanzu an gina shaguna 72 ne kacal.
Har ila yau, ya ce gwamnatin jihar tana kokari don a yanzu haka tana gina wasu shagunan zamani a garin Akwanga wanda a cewarsa idan aka kammala zai taimaka wa ’yan kasuwar a wannan bangare.
Hakazalika, Shugaban ya yi kira ga gwamnatin jihar ta taimaka musu musamman da jari don ’yan kasuwan da suka rasa jarinsu sakamakon gobarar su farfado.
“Akwai wasu bunkuna a kasar nan da suke ba wa ‘yan kasuwa bashin kudi, amma kasancewa ka’idodinsu suna da wuyar cikewa ya sa ’yan kasuwan basa iya samun rance daga bankunan,” inji shi.
Daga nan sai ya yi kira ga Gwamnan Jihar Umaru Tanko Almakura ya taimaka musu, inda ya bayyana cewa ’yan kasuwan sun fito kwansu da kwarkwata sun nuna rashin amincewansu ga yunkurin da ‘yan majalisar dokokin jihar da suka shude suka yi na tsige gwamnan kwanakin baya sun kuma zabe shi a lokacin zaben gwamnoni da ya gabata.