✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ya dace gwamnati ta bunkasa harkokin kasuwanci’

Shugaban kungiyar Dillalan Motoci ta kasa reshen Jihar Filato kuma Shugaban Kamfanin sayar da Motoci na Kega Motors ya bayyana cewa kasashen Turai da suka…

Shugaban kungiyar Dillalan Motoci ta kasa reshen Jihar Filato kuma Shugaban Kamfanin sayar da Motoci na Kega Motors ya bayyana cewa kasashen Turai da suka ci gaba a duniya, sun sami hakan ne sakamakon rungumar harkokin kasuwanci da kuma tallafi da suke samu daga gwamnatocin kasashensu.. 

Alhaji Yahaya Muhammad Kega ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu. “Dukkan gwamnatocin manyan kasashen duniya suna alfahari harkokin kasuwanci domin neman ci gaba, harkokin kasuwanci yana bunkasa tattalin arzikin kasa, musamman wajen samar da ayyukan yi ga al’umma, ” inji shi.
Ya ce domin haka ya yi kira ga gwamnati kan ta kirkiro wani shiri da zai taimakawa ‘yan kasuwa wajen bunkasa harkokin kasuwancinsu, su kafa masana’antu tare da kafa wuraren saye da sayar da kayayyakin da suke sarrafawa. “Hanyar bunkasa harkokin kasuwanci ta farko ita ce a farfado da samar da wutar lantarki da ruwa a kasar nan.
Ya ce idan aka bunkasa harkokin kasuwanci da noma mutane suka sami ayyukan yi. Kowa zai kawar da idonsa daga kan gwamnati.