Kowa da kiwon da ya karbe shi, wai makwabcin mai akuya ya sayi kura, yayin da aka san dabbobi da cin danyen nama sai ga wani mutum da shi ya kama cin danyen manan ba tare da an dafa ba a kokarinsa na neman kara tsawon rai.
Mutumin da ke cin danyen naman, ya ce yana yin haka ne don ganin tsawon lokacin da zai yi a rayuwa idan yana cin danyen nama a kowace rana.
Zuwa yanzu dai mutumin ya kwashe kwana 78 yana cin abincin da ya ce ya fi so, da suka hada da danyen naman kaji da danyen naman dabbobi da danyen kifi kuma da alama ba ya kamuwa da guba a abincin da yake ci.
Ya rubuta shafinsa na Instagram mai adireshin @ rawmeaedperiment cewa burinsa ya ci gaba da ‘cin danyen nama a kowace rana har sai ya mutu daga kwayoyin cuta.
Ya wallafa hotunan lokacin da yake cin danyen naman a yau da kullum, inda ya samu mabiya sama da dubu 60.
Yana wanke naman da danyen kwai ko madarar dabbobi.
A daya daga cikin sakonninsa na farko, mutumin wanda ya sakaya sunansa, kuma yake zaune a Amurka, ya sa danyen naman a gabansa yana cin kitse, yayin da karensa ke kallonsa cikin yunwa.
Ya dauki danyen naman a matsayin abinci, tun lokacin da ya fara jin dadin cin danyen hantar saniya da nonon rakumi.
A rana ta 33 ya shiga sha’awar cin naman sa da aka yanka, yana bayyana wa mabiyansa: “Ba na taunawa, za ku iya sa naman saniya a cikin bakinku kawai ku hadiye.”
“Akwai dadi sosai, rabin farashin nama, tabbas zai zama abincin mako-mako mai gamsarwa.’ Washegari, rana ta 34, da aka tambaye shi yadda yake ji, ya rubuta:
“Da kyau, ina sonsa har yanzu kuma ba ni da dalilin da zai sa in daina, ba wata hauka da za ta canja ni ko ta yaya.”
A rana ta 40 kuma, ya bayyana yadda ya cinye danyen nama mai nauyin Laba daya (giram 453 ko kusan rabin kilo) cikin natsuwa a cikin minti biyar.
Amma ya ce, danyen naman yana ‘girma a jikinsa’, ya yarda da dafaffen nama, ya taba dandana kadan.
A rana ta 45 ya yi wa kansa magani daga kamuwa daga cutar cin danyen nama, inda ya ce yana jin dadin abincin nasa.
Ya bayyana naman saniya da cewa ya zama daya daga cikin manyan zabin abincinsa a rana ta 76.
“Tsokar naman saniya da madarar tumaki, sun zama abincin da na fi so,” inji shi.
Ba danyen nama kadai yake ci a kowace rana ba, lokaci-lokaci yana cin dafaffen nama da dankalin Turawa ko kaza da shinkafa.
Duk da haka, yana da alkiblar irin abincinsa, yana cin dafaffen abinci kadan.