A ranar Talatar da ta gabata ce wani mai suna Deji Adenuga wanda aka fi sani da Darkar, ya banka wa gidan tsohuwar budurwarsa wuta a Titin Adetuwo, da ke garin Igbodibo a Karamar huHHukumar Okitipupa a Jihar Ondo.
Majiyar Aminiya, ta ce mutum biyar sun rasu a hadarin, yayin da mutum uku suke jinya a Cibiyar kula da mutanen da suka galabaita da ke garin Ondo Jihar Ondo.
Wata majiya ta ce Adenuga yana soyyaya da budurwar tasa ce kafin daga bisani ta ce ba ta sonsa, saboda haka sai ya harzuka ya dawo don daukar fansa inda ya banka wa dakin da iyalan suke ciki wuta.
Majiyar Aminiya ta ce “Abin da ya faru yau Talata abu ne mai ta da hankali kuma na bakin ciki. Adenuga ya shafe kusan ilahirin iyalan daga doron kasa da sassafen nan.”
“Ya fusata sosai saboda budurawa (Titi) ta ce ba ta sonsa. Kuma a kokarin daukar fansar abin da ta yi masa sai ya dauko galan din fetur ya kwara a dakin da su Titi suke barci inda ya banka wa dakin wuta. Sai ya kuskure wadda yake son hallakawa, saboda budurwa ba ta dakin a lokacin da ya banka wa dakin wuta,” inji majiyar.
Majiyar ta ce “Mutum takwas daga cikin iyalan sun kone. Biyar daga ciki sun rasu, ragowar uku kuma suna Cibiyar kula da masu mummunan rauni suna jinya.”
Majiyar ta ce wanda ake zargi ya gudu, yana tunanin mutane ba su gane shi ba.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Ondo, Femi Joseph, ya ce ’yan sanda suna bincike kan lamarin. “Muna kokarin kamo wanda ake zargi da aikata wannan danyen aiki, kuma mun fara bincike kan lamarin, nan ba da jimawa ba za mu kamo shi,” inji shi.