Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya caccaki takwaransa na Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, a kan janye takara da ya yi yayin zaben fid da gwani na jam’iyyar PDP.
Gwamna Wike, wanda yake magana a karo na farko tun bayan kayen da ya sha a zaben na fid da gwani, ya soki yadda y ace Tambuwal din ya dawo ya sake magana bayan lokacin jawabinsa ya kare a wurin taron.
- 2023: Wike ya ziyarci mahaifiyar Yar’Adua a Katsina
- Wike ya ba ’yan gudun hijirar Kaduna tallafin N200m
“Ban taba ganin yadda mutane suka yi karan tsaye wa ka’idoji ba [kamar wannan].
“Mutum ya riga ya yi magana – a lokacin da yake magana ya kamata ya ce ‘Na janye’ – bai kamata a kira shi ya dawo ba”, inji Wike.
Gwamnan na Jihar Ribas ya kuma soki wasu gwamnonin Kudu, wadanda ya zarga da cin amanar al’ummarsu.
“A matsayinka na gwamna, an je taro da kai an amince cewa mutanen [yankinka] za su karbi mulki – da in aikata haka, gwara kada a zabe ni a matsayin gwamna…
“Abin kunya – al’ummarka sun ba ka rikon amana, kuma kana ikirarin [cewa] ga abin da mutanenka suke so, amma sai da aka zo daidai wurin da za a tabbatar da [bukatar], sai ka ci amana…”
Mista Wike ya furta wadannan kalamai ne yayin wani jawabi da ya yi cikin yanayin rashin jin dadi ga al’ummar Jihar Ribas, wanda ya wallafa bidiyonsa a shafinsa na Twitter.
A cikin bidiyon ya kara da cewa, “Mun sauke namu wajibin… ba mu taba cin amanar kowa ba domin ba mu gaji cin amana ba.
“Amma abin kunya ga wadancan mutanen, wasu daga cikin gwamnonin Kudu, su ne aka yi amfani da su wajen yi mana zagon kasa.”
Sai dai duk da wannan hali na bacin rai da Gwamna Wike ke ciki, ya ce zai mara wa Atiku Abubakar baya.
Gwamna Wike ya rubuta a shafin nasa na Twitter cewa, “Na yi rantsuwa ga PDP cewa zan goya wa duk wanda ya lashe zaben fid da gwanin jam’iyyar baya, ba kuma zan yi magana biyu ba.
“Ba zai yiwu mu juya baya ga PDP ba, [don haka] za mu bayar da cikakken goyon baya ga Mai Girma Atiku [Abubakar]”.
Da ma dai tun bayan da Gwamna Tambuwal ya bayyana goyon bayansa ga Atiku, wasu mutane a Najeriya suke ganin bai yi daidai ba, musamman duba da irin gudunmawar da Gwamna Wike ya ba shi lokacin fid da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP gabanin zaben 2019.