✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Wenger zai koma Real Madrid

Rahotannin da ke fitowa sun nuna kocin kulob xin Arsenal na Ingila Arsene Wenger ya fara tunanin komawa kulob xin Real Madrid na Sifen don…

Rahotannin da ke fitowa sun nuna kocin kulob xin Arsenal na Ingila Arsene Wenger ya fara tunanin komawa kulob xin Real Madrid na Sifen don ya cigaba da horarwa.
Arsene Wenger xan kimanin shekara 67 ya kwashe kimanin shekara 20 yana horarwa ne a kulob xin Arsenal, kuma yanzu haka yana fuskantar suka daga magoya bayan kulob xin na rashin yin qoqari a kakar wasa ta bana.
Sai dai kafar watsa labarai ta The Telegraph a shekaranjiya Laraba ne ta ruwaito kocin yana faxin idan ya bar kulob xin Arsenal a qarshen kakar wasa ta bana, babu inda yake da sha’awar komawa da ya wuce kulob xin Real Madrid na Sifen.
Sai dai wani rahoto daga Sifen ya nuna kocin Madrid na yanzu Zinedine Zidane da wuya ya ajiye aiki ganin yadda yake qoqarin lashe wa kulob xin manyan kofuna a kakar wasa ta bana, idan kuma hakan ta kasance da wuya ya ajiye aiki a kulob xin.
Rahoton ya nuna kawo yanzu babu wani koci da ya kai Zidane samun nasara a kulob xin Madrid a tarihin kulob xin, inda yanzu haka ya haxa maki 72.73 daga cikin xari a wata qididdiga da kulob xin ya fitar na auna qwazon kococin da suka tava hoirarwa a kulob xin.